✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

IPMAN ta dakatar da kai mai zuwa Abuja da wasu jihohi

Ana fargabar yankewar mai a gidajen mai zuwa karshen wunin Talata.

Kungiyar Dillalan Mai ta Kasa (IPMAN) shiyyar Abuja/Suleja, ta dakatar da dakon mai zuwa birnin Abuja da Jihohin Nasarawa da Kogi.

Matakin na ranar Talata na zuwa ne bayan sabanin da ke tsakanin IPMAN da kuma Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Najeriya (DPR) ya dauki sabon salo.

Bayanai sun ce matsalar ta samo asali ne tun a ranar Litinin yayin da IPMAN wacce galibin gidajen mai mallakin mambobinta ne suka dakatar da sayar da man fetur a Suleja.

Sai dai an ci gaba da sayar da man a Abuja bisa alkawarin da DPR ta yi mata na gudanar da bincike kan matsalar zargin bukatar kudi da ake yi mata da ya saba ka’ida.

Aminiya ta samu labarin cewa a yau Talata IPMAN ta dawo da sayar da man a garin Suleja, sai dai ta jingine dakon man daga daffon zuwa jihohin uku da ma Abuja, har sai bayan zaman da za ta yi da DPR tukuna.

Wata majiya a daffon na Suleja ta shaida cewa, daffon wanda a yanzu ake amfani da shi a matsayin wurin rarraba tankunan mai zuwa yankuna hudu bayan an yi dakon man daga Kudu, a yanzu an hana fitar da man daga wajen a ranar Talata, har sai bayan zaman da bangarorin biyu za su yi.

Ta ce akwai fargabar yankewar mai a gidajen mai zuwa karshen wunin Talata, idan har lamarin ya ci gaba da tafiya a hakan.