✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Injiniya Ramatu Aminu: Burina injiniyoyi mata su yawaita a Arewa

Injiniya Ramatu Aminu Ahmed ita ce Shugabar kungiyar Injiniyoyi Mata, reshen Jihar Kano, kuma ita ce Babbar Injiniya Mai kula da Sashen Ayyukan Gine-gine da…

Injiniya Ramatu Aminu Ahmed ita ce Shugabar kungiyar Injiniyoyi Mata, reshen Jihar Kano, kuma ita ce Babbar Injiniya Mai kula da Sashen Ayyukan Gine-gine da Tsare-tsare a Jami’ar North West ta jihar Kano. Ta tattauna da Zinariya inda ta ja hankalin mata don su zama injiniyoyi.

Tarihin rayuwata
An haife ni a Unguwar Yakasai da ke Birnin Kano. Na fara makarantar firamare a Makarantar Firamaren Shahuci sannan na karasa a Firamaren Dakata a shekarar 1976. Daga nan na tafi makarantar Sakandiren Jogana inda na yi shekara uku a can. Sannan na karasa babbar sakandirena a Taura a shekarar 1987. Bayan na kammala sakandire sai na shiga makarantar CAS da ke Kano. A shekarar 1989 sai na samu gurbin karatu a Jami’ar Bayero inda na karanta bangaren gine-gine. Bayan na kammala a shekarar 1995 sai na yi aikin hidimar kasa a Hukumar Tsara Birane ta Jihar Kano (KASEPPA/KANUPDA). Daga nan sai na samu aikin koyarwa a Makarantar Sakandiren Kawaji. Ina nan ina koyarwa a shekarar 2000 sai na samu wani aikin a Hukumar WRECA ta Jihar Kano. Sai kuma a shekarar 2013 na samu canjin wani aikin a Jami’ar Jihar Kano ta North-West a matsayin Babbar Injiniya mai kula da sashen ayyukan gine-gine da gyare-gyare na jami’ar.
Abin da ya sa na zabi aikin injiniya
Zan iya cewa na samu tasirin daga wata kawata wacce muka yi karatun sakandire da ita a yanzu haka Dokta ce a bangaren Lantarki da ke Jami’ar Bayero. Tun farko na so na zama likita, sai wannan kawata ta rika nuna min muhimmancin karatun injiniya, inda take nuna mini cewa indai ina burin taimakon jama’a ne, to haka ma zan iya taimaka wa jama’a ta hanyar zamowa injiniya, har take ba ni misali da cewa idan na yi zanen madatsar ruwa duk jama’a da dabbobin da suka sha wannan ruwan zan samu lada ta wannan hanyar da sauran misalai da suka karfafa mini gwiwa na yi wannan karatu. Ada ana ganin mata, musamman Hausawa ba za su iya karatun injiniya ba, sai ga shi mun zo mun yi inda muka fita da kyakkyawan sakamako. Ba na mantawa mu ne dalibai na farko daga Kano da suka karanci aikin Injiniya a BUK. Kuma ina jin dadin wanann bangare da nake aiki.
Aikace-aikacen kungiyar Mata Injininiyoyi
Wannan kungiya an kafa ta shekaru 32 da suka wuce, sai dai mu nan Kano ba mu kafa reshenta ba sai a Shekarar 2005, inda kawata Dokta Injiniya Binta ta zama shugabar kungiyar ta farko.  Daga cikin ayyukan da muke yi mukan yi yawo makarantun sakandire na kimiyya, musamamn ma na mata inda muke nuna musu muhimmancin aikin injiniya, tare da nuna musu cewa mata ma za su iya yi, ba kamar yadda mutane ke dauka cewa aiki ne na maza kawai ba. Muna nuna musu cewa ba aiki ne na karfi ba, ba bulo ko hawa falwaya mace za ta yi don ta zama injiniya ba, abu ne na zane da kuma duba aikin ta yadda za a tabbatar masu aikin sun gudanar da shi daidai. Wani abu da ya sa muke kara zaburar da daliban nan kan karatun injiniya shi ne, ganin yadda dalibanmu na kimiyya suke makale wa neman karatun likita, wanda kuma za ka samu saboda rashin isassun gurabe a bangaren likitancin sai dai daliban su zauna haka nan ba tare da samun shiga jami’a ba, ga shi kuma can bangaren injiniyan an bar shi babu kowa. To a yanzu dai muna samun daliban suna ganewa suna shiga wannan bangare. Kuma ba wannan ne kawai inda muka tsaya ba, muna kokarin ganin cewa idan kungiya ta samu kudi sosai za mu rika daukar nauyin karatun daliban da ke son karatun injiniya, wadanda kuma iyayensu ba su da karfi. Sannan akwai shirin da muke da shi, inda za mu rika shiga kafafen watsa labarai muna  ilimintar da jama’a game da abubuwan da suka shafi rayuwarsu. Haka kuma za mu rika shiga karkara muna ilimintar da matanmu, misali game da yadda matan karkara ke debo ruwa daga kogi su sha kai tsaye, to akwai hanyar tace ruwa mai sauki ta hanyar yin amfani da gawayi da yashi wajen tace ruwa ya zama mai tsafta. Haka kuma kungiyarmu na fadakar da mata, musamamn ma’aikata inda muke nuna musu cewa duk inda mace ta samu kanta a harkar aiki, kada ta yi wasa tare da nuna kasala a tsarin tafiyar da aikinta, ta yi aiki sosai. Haka kuma wannan kungiya tana bayar da damar zuwa taron kara wa juna sani yadda za mu samu fahimtar juna da musayar ra’ayi tsakaninmu da sauran injiniyoyi mata ‘yan uwanmu a ko’ina a cikin duniya. Wani abu da ke ci wa kungiyar tuwo a kwarya shi ne, rashin kudi, kasancewar dukkaninmu mata ne masu aikin gwamnati babu wata wacce ke da wani kamfani nata na kanta, ballantana a ce tana samun kudi na daban. A yanzu haka dai mun sanya wa kawunanmu haraji da muke dan tarawa don gudanar da kungiya. Sai dai a yanzu mun fara mika kokon bararmu ga jama’a musamman ma ‘yan kwangila, kuma Alhamdulillahi muna sa ran samun wani abu daga wurinsu, domin mafi yawa daga cikinsu sun yi mana alkawarin taimako.

Nasarorin da na samu
Alhamdulillahi na samu nasarori da dama. Zan iya bugun kirji in ce ina daga cikin wadanda suka yi aikin dam din Bagauda. Na yi aikin sanya fib din ruwa wanda aka yi a zamanin mulkin Kwankwaso na farko da ake kira ‘Greater Kano”. Haka kuma ina daga cikin wadanda suka yi aikin titin da zai shigar da mutum cikin garin Tamburawa inda aka yi aikin ruwa. A yanzu ina daga cikin wadanda ke duba aikin hanya na kilomita biyar-biyar a dukkanin kananan hukumomin Kano 44.
kalubale
Babu shakka akwai kalubale wajen hada karatu ko aiki da harkar gida, Ina iya tunawa a lokacin da nake karatu a BUK a lokacin kuma ga shi ina fama da laulayin ciki, haka zan fito daga dakin jarrabawa na zo waje na yi amai na koma aji na ci gaba da rubuta jarrabawa. Babban kalubalen da zan ce na fuskanta a harkar aiki shi ne, irin yadda wasu mazan ke nuna mini wariya a matsayina ta injiniya mace. A ganinsu shisshigi ne ya sa na zama injiniya, maimakon a kara mini kwarin gwiwa. A wasu lokutan ma aikina ne wanda ya kamata ni zan yi ina ji ina gani sai a dauka a ba wani, ba wai don ba zan iya ba, sai don kawai ana ganina mace.
Yawan iyali
Na yi aure tun kafin na shiga Jami’a, haihuwata biyar sai dai a yanzu haka ina da ‘ya’ya hudu. Biyu daga cikinsu suna jami’a inda daya daga ciki yake karanta ilimin kwamfuta, na biyun kuma yana karantun zama injiniya a kan manhajar kwamfuta (Software). Sai na ukun soja yake son shiga . Akwai kuma ‘yar autata Fatima wacce ke burin karantar likita.
Buri
Ina so na ga yau an samu injiniyoyi mata masu yawan gaske, wadanda kuma suka san aikinsu, tare da samun damar yin aiki sosai. Ina da burin a ce yau ga mata injiniyoyi suna kirkire-kirkire a wannan fanni.
Shawara ga mata
Ina kira ga ‘yan uwana mata da mu rika karfafa wa ‘ya’yanmu mata game da karatun injiniya. Idan har kika san ‘yarki na sha’awar karatun wannan bangare, to ki ba ta kwarin gwiwa, a maimakon dakushe su da ake yi. Haka kuma su yara mata su dage wajen ganin sun zama abin da suke son zama a rayuwa. A gaskiya muna bukatar mata injiniyoyi masu yawan gaske daga Arewa, kasancewar takwarorinmu a Kudancin kasar nan sun yi mana fintinkau.
 Ta fuskar zamantakewa ina shawartar mata da mu zauna da mazajenmu lafiya. Haka kuma akwai bukatar mu rika kula da tarbiyyar ‘ya’yanmu, kada mu bari aiki ya dauke mana hankali mu bar tarbiyyar ‘ya’yanmu da kulawa da mazajenmu. Dole a matsayinki na mace ki tsara komai naki yadda za ki samu lokacin mijinki da an ’ya’yanki. Akwai bukatar mu rike amanar mazajenmu, duk mijin da ya bar matarsa ta fita wurin aiki, ya yarda da ita ne, to akwai bukatar mu rike wannan amanar wajen kame kanmu da sauransu. Haka kuma mata mu nemi abin yi ba lallai sai aiki ba, ko sana’a ce a cikin gida kada mu zauna zaman gulmace-gulmace, mu rika sana’a don mu taimaka wa kawunanmu da iyalanmu.