✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta hana ’yan jarida shiga cibiyar tattara sakamakon zabe a Adamawa

Ana zargin Baturen Zabe da yunkurin fifita 'yar takarar gwamna a zaben.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta yi wa ’yan jarida shamaki da shiga cibiyar tattara sakamakon zabe a Jihar Adamawa.

’Yan jaridar wadanda tun gabanin zaben Shugaban Kasa da na Gwamna aka bai wa lasisin sun yi matukar kaduwa yayin da ’yan sanda suka sanya musu shingen da ba za su bari su ketare ba.

Sai dai ’yan sandan sun ce ba haka kawai suka dauki wannan hukunci ba, inda suka labarta wa wadanda abin ya shafa cewa suna da jerin sunayen ’yan jarida da aka amince da su wanda daga baya za su kira sunayensu su shiga cibiyar tattara sakamakon zaben.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa, ana rade-radin za a sauya cibiyar tattara sakamakon zaben da ke kan tuitin banki zuwa Dougerei a birnin na Yola.

Wannan lamari dai ya janyo zanga-zanga musamman daga bangaren jam’iyyar PDP mai mulki a jihar, wadda ta sha alwashin ba za ta bari a yi wa sakamakon zaben kowace irin kitimurmura ba.

Wannan lamari dai na zuwa ne bayan da ake zargin fitar wani hoton bidiyo da aka jiyo Kwamishinan Zaben Jihar yana umartar Baturen Zaben Karamar Hukumar Fufore, Dokta Bashir Daneji da ya fifita ’yar takarar gwamnan a zaben.

Tuni dai aka soma yada jita-jita a jihar cewa akwai wasu da ke shirin tauye gaskiya a zaben.

Ya zuwa lokacin kawo wannan rahoto, wasu daga cikin jami’an tattara sakamakon zaben sun hallara a cibiyar tattara sakamakon zaben yayin da ake ci gaba da tantance kuri’un da aka kada a zaben.

Ana fafatawa ne tsakanin Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP da Sanata Aishatu Binani ta jam’iyyar APC.

Aminiya ta ruwaito cewa, a wannan Asabar ce dai ake gudanar da karashen Zaben 2023 a mazabu 2660 a kananan hukumomi 185 a cikin jihohi 24 na Najeriya.

Ana gudanar da karashen zabukan gwamna da na ‘yan majalisun dokoki a jihohin Adamawa da Kebbi.

Hankula sun fi karkata a jihohin Adamawa, Kebbi, inda ake karasa zabukan gwamnoni bayan da INEC ta ayyana su a matsayin wadanda ba su kammalu ba a zaben 11 ga watan Maris.