✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

INEC ta fara raba muhimman kayan zabe a Kananan Hukumomin Yobe

Daga can kuma za a raba kayayyakin zuwa mazabu da rumfunan zabe

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta fara raba muhimman kayan zabe a fadin Kananan Hukumomin Jihar Yobe.

Kwamishinan hukumar A Jihar, Alhaji Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a harabar Babban Bankin Najeriya (CBN) reshen Damaturu, babban birnin Jihar.

Ya ce, “Muna saura kwanaki kadan da ranar zabe, abin da muke yi a yanzu shi ne rabon wadannan kayayyaki masu muhimmanci ga jami’an zabe daban-daban.

“Daga nan ne za a raba wadannan kayayyakin ga mazabu da rumfunan zabe a fadin Jihar.

“Yayin da suke barin nan da kayan, daga nan  za su je ofisoshinsu karkashin cikakkiyar rakiyar jami’an tsaro da sojoji da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.

“Wannan shi ne don tabbatar da cewa Kayayyakin sun isa lafiya don ci gaba da rarrabawa ga mazabun da rumfunan zaben da ke jihar,” in ji shi.

Kwamishinan ya kuma yi kira ga duk wadanda suka cancanci kada kuri’a da su fito gaba daya domin zaben mutanen da suke so a ranar zabe.

Ibrahim Abdullahi ya ce, “Kiran ya zama wajibi domin idan ba su fito ba, za su iya zama da shugabannin da ba sa so su jagorance su.”