Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta fara raba muhimman kayan zabe a fadin Kananan Hukumomin Jihar Yobe.
Kwamishinan hukumar A Jihar, Alhaji Ibrahim Abdullahi ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis a harabar Babban Bankin Najeriya (CBN) reshen Damaturu, babban birnin Jihar.
- Yadda karancin kudi ya takaita tafiye-tafiyen ’yan Najeriya lokacin zabe
- Sheikh Dahiru Bauchi ya bukaci mabiyansa zu zabi Atiku
Ya ce, “Muna saura kwanaki kadan da ranar zabe, abin da muke yi a yanzu shi ne rabon wadannan kayayyaki masu muhimmanci ga jami’an zabe daban-daban.
“Daga nan ne za a raba wadannan kayayyakin ga mazabu da rumfunan zabe a fadin Jihar.
“Yayin da suke barin nan da kayan, daga nan za su je ofisoshinsu karkashin cikakkiyar rakiyar jami’an tsaro da sojoji da ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
“Wannan shi ne don tabbatar da cewa Kayayyakin sun isa lafiya don ci gaba da rarrabawa ga mazabun da rumfunan zaben da ke jihar,” in ji shi.
Kwamishinan ya kuma yi kira ga duk wadanda suka cancanci kada kuri’a da su fito gaba daya domin zaben mutanen da suke so a ranar zabe.
Ibrahim Abdullahi ya ce, “Kiran ya zama wajibi domin idan ba su fito ba, za su iya zama da shugabannin da ba sa so su jagorance su.”