Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta ci gaba da karba da tattara sakamakon Zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar Asabar.
Wannan dai na zuwa ne duk da zanga-zangar da ta barke a Abuja, babban birnin kasar kan bore da wasu jam’iyyu da masu ruwa da tsaki ke yi kan zaben.
- APC ta yi martani kan bukatar soke zaben ranar Asabar
- Sayen kuri’u: Fintiri ya dakatar da ayyukan kungiyoyi masu zaman kansu a Adamawa
Tun a ranar Lahadin da ta gabata ce dai INEC ta soma karba da tattara sakamakon zaben a Cibiyar Taro ta Kasa ICC da ke Abuja.
Sai dai bayan tashi daga aikin tattara sakamakon zaben da misalin karfe 10:00 na daren ranar Litinin, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya dage wannan aiki zuwa karfe 11:00 na safiyar wannan Talatar.
A cewar Farfesa Yakubu, hakan zai bai wa sauran jami’an da hukumar ta ratayawa nauyin gabatar da sakamakon na ragowar jihohin wadataccen lokaci su cika aiki.
Sai dai kuma a sanarwar da ya fitar, Kwamishinan Wayar da Kai na INEC, Festus Okoye, ya ce karba da tattara sakamakon zaben zai ci gaba da gudana da misalin karfe 2:00 na ranar Talatar.
Mista Okoye ya ce duk da cewa akwai sakamakon zaben jihohi biyar da ke kasa kuma sun shirya gabatar da shi, zai fi kyautuwa a samu sakamakon zaben jihohi 10 da ke kasa yadda za a dauki lokaci ana gabatarwa gabanin tafiya hutun rabin lokaci.
Aminiya ta ruwaito cewa, duk da wannan sanarwa, aikin karba da tattara sakamakon zaben bai ci gaba da gudana ba sai bayan karfe 4:45 na Yammacin wannan Talatar
An dai dawo ci gaba sa karba da tattara sakamakon zaben ne da Jihar Neja.
Haka kuma, ana ci gaba karba da tattara sakamakon zaben ne duk da wasu kungiyoyi sun bazama a birnin na Abuja suna bore kan zaben.
A yayin da wasu bangaren ke kiraye-kirayen da a soke zaben a sake gudanar da wani sabo saboda rashin amfani da na’urar tantance masu zabe ta BVAS a wasu rumfunan zaben, wasu kuwa boren nasu na adawa da hakan ne.
Tuni dai an gabatar da sakamakon zaben jihohi akalla 13, inda jam’iyyun da sake sahun gaba suke rarraba tarin kuri’un da aka kada a tsakaninsu.