✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta bukaci a gurfanar da Kwamishinan Zaben Adamawa a Kotu

INEC ta bukaci Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya gurfanar da REC na Adamawa a gaban kotu kan azarbabin sanar da sakamakon zaben Adamawa

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bukaci Shugaban ’Yan Sandan Najeriya ya bincika tare da gurfanar da Kwamshinan Zabe na Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunus Ari, a gaban kotu kan sanar da sakamakon zaben gwamnan jihar ta haramtacciyar hanya.

INEC ta bukaci hakan ne bavan ganawar sirri da Kwamishinoninta suka yi a hedikwatar hukumar da ke Abuja ranar Talata kan rudanin da Barista Hudu ya haddasa.

Game da makomar sakamakon zaben kuma, INEC ta ce “Nan gaba jami’in jattara sakamakon zaben gwamnan jihar Adamawa, zai sanar da lokacin da za a ci gaba da tattara sakamakon.”

Amma shi Hudu, a “gagguta binckar sa domin tabbatar da ganin an gurfanar da shi a gaban kuliya.”

Sanarwar hukumar ta bayan ganawar sirrin ce ta za ta “sanar da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya abin da Kwamishina Zaben ya aikata, saboda ofishin ya dauki matakin da ya dace a kansa.”

A ranar Lahadi ne Barista Hudu ya yi gaban kansa — a bayan idon jami’in tattara sakamakon zaben, ya sanar cewa Aisha Binani ta APC ta yi nasara.

Hudu ya yi haka ne a yayin da ake jiran karbar sakamakon kananan hukumomi 10 na jihar a zaben da aka karasa, kasancewar INEC ta ayyan wanda aka fara gudanarwa a ranar 18 ga watan Maris a matsayin wanda bai kammala ba.

Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam’iyyar PDP yana neman komawa kan mulki a karo na biyu a zabe, a yayin da Sanata Aisha Binani ta APC ke neman kai bantenta. Karo na biyu ke nan da take zawarcin kujerar gwamnan jihar.