Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) na sa ran a ranar Lahadi za ta bayyana da sakamakon karshe na zaben Gwamnan Jihar Ondo.
Kwamishinar Zabe na Kasa Farfesa Anthonia Simbine, ta sanar da haka da yammacin Asabar lokacin da take cewa INEC ta sanya kashi 70 na sakamakon zaben a shafinta na tattara sakamakon zabe a intanet.
- Zaben Ondo: Akeredolu na kan gaba a sakamakon kananan hukumomi 10
- Zaben Ondo: Dan takarar PDP ya koka kan matsalar na’urar tantance masu zabe
Farfesa Anthonia ta ce duk da haka akwai yiwuwa a samu jinkirin isowar alkaluman zabe daga wasu yankuna da ke tsallen koguna.
Tun a ranar Asabar cibiyoyin hukumar na tattara sakamakon zabe a Kananan Hukumomin Jihar 18 suka fara tattara alkaluman mazabu tare da fitar da sakamakon kananan hukumomin.
Daga bisani suna mika sakamakon ga babbar cibiyar tattara sakamon zaben hukumar a Jihar wadda ita ce za ta sanar da sakamakon karshe.
Zuwa lokacin rubuta wannan rahoto INEC ta sanar sakamakon zaben daga kananan hukumomin Akoko ta Kudu maso Gabas, Akoko ta Kudu maso Yamma, Akoko ta Arewa maso Gabas, Akure ta Kudu, Akure ta Arewa, Ese Odo, Idanre, Ifedore, Ile Oluji, Irele, Okitipupa, Ondo ta Gabas Ose da kuma Owo.
Rahotanni daga rumfunan zabe sun nuna kowanne dukkannin manyan ’yan takara a zaben ya lashe zabe a mazabarsa.
Manyan masu fafatawa a zaben sun hada da Gwamna Rotimi Akeredole na Jam’iyyar APC da ke neman wa’adi na biyu, Maitamakin Gwamna Agboola Ajayi mai takara a jam’iyyar ZLP, da kuma mista Eyitayo Jegede da ke neman kujerar a karkashin babbar jam’iyyar adawa ta PDP.