✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ba ta shiryawa zaben Edo ba – Obaseki

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya koka kan yadda Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da zaben gwamna a jiharsa. Obaseki ya bayyana rashin…

Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki, ya koka kan yadda Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta gudanar da zaben gwamna a jiharsa.

Obaseki ya bayyana rashin dadi dangane da yadda aka rika samun cikas wajen amfani da na’urar ‘card reader’ mai tantance katin masu zabe a rumfunan zabe da dama a jihar.

Yayin ganawa da manema labarai bayan jefa kuri’arsa a rumfar zabe mai lamba 19 a gunduma ta 4 a karamar hukumar Oredo da ke jihar, Gwamnan ya ce ya shafe sama da sa’a daya a kan layi jefa ya kuri’a saboda rashin saurin na’urar tantance masu zaben.

Ya ce “bayan shafe sa’o’i da dama a kan layi saboda cikas da na’urar tantance masu zaben ta kawo, shi ya nuna cewa Hukumar INEC ba ta shiryawa zaben ba.”

“Na yi tsammanin cewa INEC za ta yi wa wannan zaben wani shiri na musamman.”

“Na shafe fiye da sa’a daya da rabi a kan layi kafin na samu damar kada kuri’ata, ban ji dadin lamarin ba,” inji shi.