Wasu mazauna Kudancin Indiya, sun yi wa wasu kwadi bikin aure na musamman don neman tsari daga karancin ruwa da fari da amfanin gonarsu ke fama da shi.
Wanda ya shirya auren kwadin mai suna Deepak Das, ya ce manoma a yankin na fuskantar matsalar rashin ruwa da sauran matsalolin da suka shafi amfanin gonakinsu.
- Hare-Haren Jirage da Ambaliya Sun Sa ’Yan Boko Haram ISWAP Gararamba
- Yadda dan China ya kashe ’yata a gidanmu —Mahaifiyar Ummita
“Manoma suna fuskantar matsaloli masu yawa a dalilin fari, shi ya sa muka shirya wannan biki na musamman,” inji shi.
Lamarin ya fi tsamari a Jihar Assam da ke Indiya, inda manoma da mazauna jihar ke fuskantar matsanaciyar fari.
Bayan daura wa kwadin aure sun sake su don ci gaba da yin rayuwarsu tare da cin angwanci.
Wata da ta halarci bikin auren mai suna Cheena Bora, ta ce “Mun yi musu wanka daya bayan daya, sannan muka yi musu sadaukarwa.
“Mun dauke su zuwa wurin bauta, muka zagaya da su kamar yadda doka ta tanada, daga karshe muka sake su a cikin ruwa,” inji ta.
A cikin bidiyon da tashar talabijin ta Al Jazeera ta wallafa a shafinta na YouTube, ta ce kwadin da suka angwancen ba su ba ne na farko da aka fara daura wa aure a yankin.
Sai dai mazauna yankin sun ce ba kasafai zamantakewa take dorewa ba a tsakanin kwadin.
A shekarar 2019, wasu mazauna wani kauye a Indiya sun raba auren wasu kwadi sakamakon ambaliyar ruwa da aka samu a yankin.