Jakadan Indiya a Najeriya, Shri Balasubramanian, ya ce kasarsa za ta bai wa ’yan Najeriya 500 tallafin karatu a bana.
Balasubramanian ne ya bayyana a ziyararsa ga shalkwatar Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa (NAN) da ke Abuja, cewa za su fadada bangaren nazarin aikin jarida a fitattun jami’o’insu.
- Ba na cikin hayyacina lokacin da Ummita ta rasu —Dan China
- Ambaliya: Gwamnatin Tarayya Ta Tallafa wa Manoma 200 A Gombe
“Akwai shirin da muke yi don dibar wasu ’yan jarida daga Najeriya zuwa Indiya, ba don su yi wani kwas ba, sai don kai ziyarar gani da ido, don nuna musu yadda Indiyawa ke tafiyar da siyasarsu.
“Ba kuma iya su kadai za mu diba ba, har da wasu da suka fito daga sauran kasashen yankin Yammacin Afirka.
“Za kuma mu bai wa ’yan Najeriya 500 tallafin karatu kamar yadda muka saba yi duk shekara, a bangaren ikin jarida da sauransu. Amma sai a watan Marisa, lokacin da sabuwar shekarar karatun Indiya za ta fara”, in ji shi.
Jakadan ya kuma yaba da kyakkyawar alakar da ke tsakanin kasasen biyu, tare da bayyana cewa Indiyan za ta ci gaba da kara yaukaka alakar, musamman ta fuskar kiwon lafiya.