Gidauniyar Daily Trust da haɗin guiwar ta MacArthur sun gudanar da taron horar da ’yan jarida daga jihohi shida na Arewa maso Gabas kan bibiyar kasafin kuɗi da bincike.
Taron, na kwana uku ya tattara fiye da mahalarta 25 daga cibiyoyin watsa labarai daban-daban, na gwamnati da masu zaman kan su wanda horon ɗaya ne daga cikin Ayyukan Al’umma (CSR) na kamfanin Media Trust Group, tare da goyon bayan Gidauniyar MacArthur.
A jawabinsa na maraba, Shugaban Gidauniyar Daily Trust Malam Bilya Bala, cewa ya yi wannan horon ya zama dole don ƙara basirar ’yan jarida wajen bibiyar kasafin kuɗi tun daga asali har zuwa lokacin aiwatarwa.
Bala ya ce aikin ’yan jarida ne su wuce tsayawa neman bayanan gwamnati ta ce dole su tashi su bibiyi kuɗin su gano yadda ake aiwatar da albarkatun da aka yi kasafi a kansu da kuma abin da aka tsara su yi.
- NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Matsakaicin Karfi A Najeriya?
- Gwamnatin Nijeriya ta yi sakaci kan kisan Sarkin Gobir — Atiku
Ya ce, “Kullum ku riƙa sanar da mutane yadda aka aiwatar da kasafin kuɗi yayin da kuke riƙe gwamnati da alhakin duk alƙawuran da aka yi, da kuma matakan aiwatarwa, tare da shaidu.”
Ya ƙara da cewa Media Trust tana ware wani ɓangare na ribarta don bayarwa a matsayin taimako ga wasu nau’ikan marasa galihu.
A nasa Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Gombe, Mijinyawa Arɗo Tilde, wanda ya wakilci gwamnan, ya ce yawancin ayyukan gwamnati ana aiwatar da su ne bisa ga buƙatun da aka gano ta hanyar haɗin gwiwa da ƙungiyoyin fararen hula da sarakunan gargajiya da kuma tarukan jama’a.