A ranar Litinin da ta gabata ce Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai shari’a Binta Murtala Nyako ta dage shari’ar jagoran masu rajin kafa kasar Biyafra Nnamdi Kanu zuwa ranar 21 ga Oktoba mai zuwa.
A ranar Litinin din ce aka so a ci gaba da sauraron shari’ar sai dai rashin kai shi kotun daga bangaren jami’an tsaro ya sa aka dage shari’ar.
- Yadda rashin fahimtar yanayin mata ke jawo mutuwar aure
- Yadda gayyatar da Majalisa ta yi wa Alkalin Alkalan Kano ta tada kura
A karshen watan jiya ne, Kotun Tarayya ta bayar da umarnin a tsare jagoran ’yan a-waren, bayan masu gabatar da kara sun sake gurfanar da shi a gabanta, sakamakon kamo shi daga kasar waje.
Gwamnatin Tarayya tana tuhumarsa da laifuffuka 11, ciki har da cin amanar kasa da ta’addanci, da mallakar miyagun makamai da kuma kokarin tunzura jama’a su haifar da yamutsi.
Lauyoyin gwamnati da na jagoran ’yan a-waren sun hallara a kotun. Sannan wadansu masu fafutika sun yi gangamin goyon bayan Nnamdi Kanu a kofar Babbar Kotun, inda ’yan sanda suka kama da dama ciki har da mawallafin jaridar Sahara Reporters da ake bugawa a Intanet, Omoyele Sowore inda daga bisa aka sako shi.
Ran Alkalin ya baci
A zaman kotun na ranar Litinin, Mai shari’a Binta Nyako, ta nuna bacin ranta kan rashin gabatar da Kanu a kotun.
Ta yi gargadin cewa ba za ta sake yarda da halin da aka nuna na kin gabatar da shi a gaban kotu ba.
Tun farko lauyan Kanu, Barrister Ifeanyi Ejiofor, ya yi korafin cewa hukumomin kasar sun ki barinsu su gana da wanda ake tuhumar.
A karshen watan Yuni ne Ministan Shari’a Abubakar Malami, ya sanar da kama Kanu, wanda ya tsere daga kasar nan.
Zuwa yanzu hukumomi ba su bayyana kasar da aka kamo jagoran ’yan a-waren na Biyafra ba, sai dai Kamfanin Dillacin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce wani Minista a Ma’aikatar Harkokin Wajen Birtaniya ya bukaci Najeriya ta yi musu bayani a kan haka.
Shi dai lauyan da yake kare Nnamdi Kanu ya ce an kama shi ne a Kenya, kuma an azabtarda shi tsawon kwana takwas kafin a mika shi ga hukumomin Najeriya.
Ofishin Jakadancin Kenya a Najeriya ya musanta wannan zargi, sai dai Kungiyar IPOB mai fafutikar kafa kasar Biyafura ta nace a kan haka, kamar yadda muka kalato daga BBC.
Matashiya
A watan Afrilun 2017 aka bayar da belin Kanu bisa dalilai na rashin lafiya, sai dai ya tsere daga kasar nan.
Sharuddan belin su ne sai Kanu ya gabatar da mutum uku wadanda za su tsaya masa kuma kowane ya kasance yana da Naira miliyan 100.
A watan Maris na 2019 ne Babbar Kotun Tarayyar ta soke belin da ta bai wa Kanu saboda zargin tsallake belin sannan ta umarci hukumomin tsaro na ciki da wajen Najeriya su kamo mata shi.
Daga bisani jami’an tsaron Najeriya suka ayyana IPOB a matsayin Kungiyar ’Yan Ta’adda.
Lauyoyin Nnamdi Kanu sun kai kuka ga Tarayyar Afirka
A wani labarin lauyoyin jagoran ’yan a-waren sun ce sun fara daukar matakin shari’a a kan Gwamnatin Tarayya da Kenya a Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Tarayyar Afirka (AU).
Sun bukaci kasashen biyu su yi bayani dalla-dalla a kan zargin tasa keyar wanda suke karewa zuwa gida ba tare da bin ka’idojin da suka dace ba.
A wata sanarwa da babban lauyan Kanu, Alloy Ejimako ya fitar, ya ce sun kai batun gaban AU ne saboda dukkan kasashen biyu mambobi ne na Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Tarayyar Afirka.
Lauyoyin Kanu sun bukaci a mayar da shi kasar Kenya kuma a matsayin dan Birtaniya, tare da zargin cewa kama shi da aka yi ya saba wa doka.
Nnamdi Kanu yana da takardar zama dan Birtaniya, kuma har yanzu babu cikakken bayani a kan yadda aka taso shi zuwa Najeriya a watan jiya. Gwamnatin Kenya ta musanta hannu a kama shi da mayar da shi Najeriya.