’Yan Majalisar Wakilai 50 sun aike wa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu wasikar neman ya saki shugaban kungiyar ta’addanci ta IPOB, Nnamdi Kani.
Honorabul Mohammed Jajere ya tabbatar wa Aminiya goyon bayansa ga bukatar a saki Namadi Kanu, wanda kungiyarsa ta IPOB ke neman ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Biafra.
A halin yanzu dai Gwamnatin Tarayya tana gurfanar da shi a kan laifukan ta’addanci da kuma cin amanar kasa.
Mohammed Jajere ya bayyana cewa sakin Nnamdi Kanu zai sa samu wanzajjen zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas da ma Najeriya baki daya.
- NAJERIYA A YAU: Alamomin Da Ke Nuna Alhaji Ya Yi Hajji Karbabbe
- Abba ya umarci jami’an tsaro su kawo ƙarshen faɗan daba a Kano
Ya ce wasikar da ’yan majalisar, karkashin kungiyarsu ta kishin Najeriya ya ce, suka rubuta wa Tinubu ta “ba da shawarar tattaunawa da Gwamnatin Tarayya domin samun zaman lafiya mai dorewa.
“Shi ya sa muke rokon Shugaba Tinubu ya amince a yi sulhu a wajen kotu domin a shawo kan lamarin.
“Ta wayar tarho aka sanar da ni abin da wasikar ta kunsa kuma na amince, don a samu zaman lafiya,” kamar yadda ya shaida wa wakilinmu ta wayar salula.
A wasikar da ’yan majalisar suka rubuta wa Tinubu ranar 19 Yuni 3024, sun bukaci ya yi amfani da ikonsa da kundin tsarin mulki ya ba shi, ya umarci Ministan Shari’a ya janye karar Nnamdi Kanu, a sasansta a wajen kotu.
Sun kuma ba da misali da cewa kafin yanzu Tinubu ya ba da damar yin irin wannan sulhu da Omoyele Sowore da kuma Sunday Adeyemi (Igboho) wadanda su ma gwamnatin ta zarga da laifin cin amanar kasa.
Mambobin majalisar sun kuma bukaci a samar da shirin samar da zaman lafiya domin tabbatar da aminci a yankin Kudu maso Gabas da ma Najeriya baki daya.
Wasikar neman Tinubu ya saki Nnamdi Kanu
Wasikar da ’yan majalisar suka rubuta wa Tinubu ta ce: “Muna rokon ka da ka umarci Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya ya yi amfani da ikon ofishinsa ya saki Nnamdi Kanu tare da janye karar sa a gaban kotu.
“Mun yi imanin cewa tun tuni ya kamata a yi hakan, wanda kuma zai bude kofar samun zaman lafiya, kawo cigaba tare da tafiya da kowane bangare.
“Hakan zai magance matsalar da ta haifar da kokensu, musamman ma idan aka yi gyara ga kundin tsarin mulki.
“Yin hakan zai kawo hadin kan kasa tare da magance matsalolin tsaro da na siyasa da na tattalin arziki a yankin Kudu maso Gabas, wanda kuma zai bayu ga amincewar al’ummar yankin su shiga a tattauna da su kan al’amuran da suka shafi kasar nan.
“Sakin Nnamdi Kanu zai kawo karshen rikici da tsahin hankali a yankin sannan ya kawo wa yankin cigaba da bunkasar tattalin arziki;
“Musamman a wannan lokaci da kasar nan take fama da matsalolin rashin ayyukan yi da na rashin tsaro da fatara da yunwa da rashin kwanciyar hankali.”