Tauraron dan wasan Paris St. Germain, Lionel Messi ya bayyana cewa, yana fatan komawa Barcelona amma a matsayin Darektan Wasanni kungiyar nan gaba a rayuwarsa.
Wannan na zuwa ne bayan dan wasan na Argentina mai shekaru 34 ya raba gari da Barcelonar a cikin watan Agustan da ya gabata tare da komawa PSG ta Faransa.
- Tallafin man fetur ya lakume Naira biliyan 864 a wata 8
- Najeriya A Yau: Yadda jami’ai ke ‘agaza wa’ masu fasa-kwauri
A hirar da ya yi da jaridar Sport ta Spaniya, Messi wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or shida ya ce “A ko yaushe ina cewa zan so in taimaka wa kungiyar.
“Idan akwai yiwwar, zan so in sake ba da gudummawa saboda kulob ne da nake so kuma zan so ya ci gaba da samun nasara da bunkasa, kuma ya ci gaba da kasancewa daya daga cikin kungiyoyin kwallon kafa mafi kyau a duniya.”
“Duk da cewa ban fara tunanin ritaya ba tukunna, zan so na zama daraktan wasanni a Barcelona a wani lokaci.
“Ban sani ba ko hakan zai kasance a Barcelona ko a wani wuri da ban. Idan akwai damar, zan so in koma in ba da gudummawa.
Ya kara da cewar “Wannan shi ne abinda matata ke so kuma abin da nake so.
“Ban san lokacin da kwantiragina zai kare da PSG ba amma za mu koma Barcelona da zama.”