Dokta Maryam Abubakar Koko daya ce daga cikin sanannun mata a Jihar Sakkwato da suka kware wajen inganta rayuwar mata da samar masu hanyar dogaro da kai da wayar da kansu kan matsalolin rashin sana’a. Ita ba ta da buri da ya wuce inganta rayuwar mata. Aminiya ta tattauna da ita don sanin tarihinta.
Tarihi
Sunana Dakta Maryam Abubakar Koko, an haife ni a shekarar 1975 mahaifana Habiba Abubakar Koko da Abubakar Koko. An sa ni firamare ina da shekara 7 a garin Koko ina cikin aji hudun na Firamare na sauke Alkur’ani, na yi karance-karancen litttafai kafin na shiga Sakandare. Abin da ya kara sa ni alfahari da mahaifina Allah ya jikansa da rahama ya bar ni na koyi addini da al’adata da sanya min son sana’a da yin dogaro da kai. Tun ina ‘yar shekara tara na fara yin sana’a kuma tun a lokacin nake ganin alfanun abin. Bayan na gama karamar sakandare sai aka bani takardar cikewa don zabar fannin da nake son karantawa a babbar Sakandare. Gidanmu suna da sha’awar in karanci fannin ilmin kimiya ni kuma ina da shaáwar karatun ilmin Sana’a , a karshe dai mahaifina ya ce abar ni in karanci abin da nake so ya karfafa mini gwiwa, dana kammala sakandare na samu gurbin karatun digiri na farko a jami’ar Usman Dan fodiyo da ke Sakkwato a fannin ilmin Kasuwanci, anan na yi digiri na biyu da na uku. A yanzu ni babbar malama ce (senior Lecturer) a jami’ar. A fannin ilmin kasuwanci na kai matakin Dakta ina fatan zama Farfesa, ina kasuwanci a da koyar da sana’a a zahiri.
Shin mata na iya hada karatu da Aure?
Kwarai zai yi wu, a karatuna gaba daya da aure da ‘ya’ya har da ‘yan biyu na yi shi, ban kuma watsar ba. A rayuwa in kace za ka yi abu to za ka iya, aure haihuwa ba ya hanawa mata karatu ka dai yi tsari mai kyau ka bar wa Allah komai. Ina renon ‘yan biyu maza suna da shekara daya da rabi Babansu ya rasu wannan yana iya tankwashe mutum musamman matanmu in sun rasa miji sai su yanke kauna ka gansu suna roko nan da can. To ni gaskiya rasuwar kara min kaimi ta yi na ga ga yara biyu kanana wa zai kula min da su ga shi duka shekaruna ba su wuce 30 ba. Da taimakon mahaifana da aikin da nake yi da kasuwanci na rika kulawa da su, har na sake wani aure na auri Farfesa da ya San girmana da na yarana da aikina ya kuma karfafa ni saboda fahimtar juna da muke da ita.
Kalubalen da kika fuskanta
Gaskiya rasuwar mijina kwatsam babban kalubale ne gare ni duk da na san mutuwa ba ta bayar da salahu. Sauran kananan kalubale na can da nan ba’a manta su amma sukan zo su wuce. Rashin mahaifina mai kara mini kwarin gwiwa don samun nasara rayuwata shi ma kalubale ne. A harkar kasuwancina ina da gidan abinci ana yi abu ya zo ya lalace, ba yanda ka’iya gobe za ka sake daura wani. Bayan matsalar masu kula maka, don matan Hausawa ba su yin aikin, ni ma na shiga ne don ina da sha’awan fitowa da abu na zamani. A tafiye-tafiye na na ga abubuwan kwalama da yaro ke so babu shi anan, matanmu ba su sana’a sai ta gida amma abun ya fara canzawa.
Ko burinki na kuruciya ya cika?
Wani ya cika wani ko da saura, ina son in yi sana’a a lokacin ina karama, ga shi ina yi yanzu amma akwai in da nake son in kai a harkar. Waton sahun gaba a farkon mata 10 masu sana’a a Nijeriya, amma dai yanzu na samu karbuwa a sana’ata, ina son na zama gaba sosai wurin biyan bukatun abokan huldata. Ina burin zama Farfesa a fanin ilmin kasuwanci ga shi ina kusa na cika burina.
Bayan ba ki nan me kike son a tuna ki da shi?
Abubuwa da dama in kana karantarwa kana son barin wani abin tunawa da kai da za a rika yi maka addu’a, ina son a rika tunawa da ni kan taimakon al’umma da samar masu hanyoyin dogaro da kai, ina kan yi hakan a hankali, ina koyi da sunnah Annabi da shi nake koyi gaba daya a rayuwa.
Iyali
Yarana 7 mata hudu maza 3, duk yarana suna makaranta diyata ta farko tana karatun ilmin gwaje-gwaje(Lab science) ta biyu tana karatun Ingilishi(English) ta ukku tana karatun kimiyyar Physics duk a jami’ar Danfodiyo. Sauran ma suna yi a fannoni dabam daban kuma ba wadda ba ta sana’a cikinsu, suna kasuwancinsu tare da karatu lokaci daya. Su ne ke da tunaninsu ni kawai shawara ce tawa don ina ilmin kasuwancin mata ta yanda za a taimaki mata, ina bayar da shawara ga Bankin masana’antu(Bank of Industry), da horar da masu son yin sana’a da makamantan haka.
Shawara ga mata
Mata muna baya kwarai a fannin sana’a mun sani muna da nauyi kanmu ya kamata duk wata basira da ki ke da ita ki gwada ki shirya kar ki yi saku-saku da ilmin tarbiyantar da yaranmu. Matsalar mutuwar aure har da rashin sana’ar mata na ciki, bayan sakaci sosai ga uwaye mata a wannan yanayi mata matasa sun fi maza shaye-shaye, suna lalata kwakwalwarsu kullum a barci babu tunanin abin da mutum zai yi mai fitar da shi. Tarbiya tana hannun iyaye a duniya an baki yara idan ba ki rene su ba wa ki ke son ya rene su bayan ba ki nan?.