✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina rokon ’yan Najeriya su bari tsarin canjin kudi ya yi aiki —Emefiele

Wahalar da ke tattare da manufar a halin yanzu ta wucin-gadi ce.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya roki ’yan Najeriya da su bari sabon tsarin canjin Naira ya yi aiki don cimma manufarsa.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Fadar Shugaban Kasa, jim kadan bayan ganawarsa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a Abuja.

Emefiele ya ce wahalar da ke tattare da manufar a halin yanzu ta wucin-gadi ce, inda ya nuna cewa manufar za ta tabbatar da kudirin gwamnati na dakile cin hanci da rashawa da kuma bunkasa tattalin arziki.

Ya ce: “Gaskiya ita ce dukanmu hidima muke yi. Muna yi wa ‘yan Najeriya hidima ne.

“Antoni-Janar ya yi magana kan wannan al’amari kuma Shugaban Kasa ya yi nasa aikin a safiyar yau (Alhamis).

“Kirana ga ‘yan Najeriya shi ne kawai mu bari wannan tsari ya yi aiki yadda ya dace.

“Wannan manufar ita ce hanya daya da za ta rage matsalar cin hanci da rashawa da tabarbarewar tattalin arziki.

“Haka kuma, wamnan manufar tana tafiya ne don warware wasu matsalolin tattalin arziki da matsalar tsaro a kasar nan.

“Don haka wadannan batutuwa guda uku su ne jigon wannan kudiri da gwamnati ta kawo ta hanyar manufofin nan. Mu bari tsarin ya yi aiki.

“Muna kukan wahala amma ta wucin-gadi ce, ina tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ribar da Najeriya za ta samu idan tsarin ya yi aiki ba kadan ba ce.”

A jawabinsa a safiyar Alhamis, Buhari ya bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsohuwar takardar kudi ta N200 har zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.

Shugaban ya ce manufar za ta takaita siyan kuri’a a lokacin zabe.

Da yake tsokaci, Emefiele ya ce, “Shugaban Kasa ya bayar da umarninsa kuma na gana da shugabannin bankunan kasuwanci 15 a safiyar yau, inda muka ba su umarni kan yadda za su samu tsofaffin takardun N200 da yadda za su fara aiki nan take a yau.”