✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina rera waka cikin harsuna uku – Hassan Saleh

Hassan Saleh wani matashin mawaki ne da yake rera wakokinsa cikin harsunan Hausa da Turanci da kuma Fulatanci. Aminiya ta samu zantawa da shi ga…

Hassan Saleh wani matashin mawaki ne da yake rera wakokinsa cikin harsunan Hausa da Turanci da kuma Fulatanci. Aminiya ta samu zantawa da shi ga kuma yadda hirar ta kasance:

Ahmed Ali, a Kafanchan

Wane ne Hassan Saleh?
Ni mutumin garin Kachiya ne cikin karamar Hukumar Kachiya da ke Jihar Kaduna. Shekaruna 26 kuma ni Bafulatani ne.
Wadanne irin wakoki kake yi?
Babu irin wakar da ba na yi, kama daga ta fadakarwa zuwa ta soyayya.
A wane lokaci ka fara yin wakoki?
Na fara rubuta waka ne a shekarar 2006 amma ban fara rerawa a situdiyo ba sai a 2011.
Me ya ja ra’ayinka ka fara rubuta wakoki?
Tunani kawai na zauna na yi game da abubuwan da ke faruwa a rayuwarmu ta yau da kullum, shi ne na fara tunanin ta yaya zan isar da sakona ya kai ga kunnuwan matasa musamman? Shi ne sai na ce bari in fara gwada yin waka, dayake na ga matasa sun fi raja’a ga sauraron wakoki.
Ga ka Bafulatani, da wane harshe kake rera wakokinka?
Ina rubuta waka da rerawa da harsunan Hausa da Turanci da kuma Fulatanci.
Wane irin jigo ne kake gina wakokinka a kai?
Ina yin wakokina ne kan fadakarwa game da abubuwan da ke faruwa yau da kullum sai kuma bayyana tarihi kuma ina taba wakokin soyayya. Kusan dai ba fannin da ba na rubuta waka a kai.
Wadanne wakoki ka fi alfahari da su cikin wadanda kake yi da harsunan da ka ambata?
Gaskiya an fi sauraron wakokina na Fulatanci, domin za ka ji ana ta kira na daga wurare daban-daban, wadansu ma suna tambayata yaya nake yi in rubuta waka da Fulatanci kuma in shiga situdiyo in rera?
Ko ka taba samun wata kyuata a harkar waka?
Ban taba samu ba.
Yaya batun dillancin wakokin naka?
Gaskiya ban taba daukar faifan wakokina na sayar ba, sai dai ina so in samu ’yan kasuwa masu amana mu fara gwadawa.
Akalla wakokinka sun kai guda nawa?
Sun kai guda goma zuwa yanzu.
Mene ne kiranka zuwa ga gwamnati?
Kirana kawai shi ne, gwamnati ta rika tallafa wa matasa saboda za ka ga wani Allah Ya hore masa baiwa amma rashin samun wanda zai tallafa masa sai ya kasa tabuka komai a cikin al’umma.
Wadanne matsalolin da kake fuskanta a harkar waka?
Matsalar kudi ce kawai ta yadda zan rika fitar da wakoki a duk lokacin da na rubuta na rera.