Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, ya jaddada kudirin cewa ba ya da wani shiri na sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa ta APC mai mulki a Jihar.
Hakan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan gangamin da aka gudanar na karbar Gwamnan Jihar, Muhammad Bello Matawalle da ya sauya sheka daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC.
“Zan ci gaba da kasancewa tare jam’iyyarmu da kuma mutanen da suka goya mana baya a lokacin da muke bukatarsu,” a cewar Mataimakin Gwamnan.
Ya ce ya yanke shawarar ci gaba da zama a jam’iyyar ta PDP bayan dogon nazari da kuma tuntubar abokai, ‘yan uwa da makusanta a jam’iyyar.
Mataimakin Gwamnan wanda da ne ga tsohon Mai Bayar da Shawara kan Harkokin Tsaron Kasa, Janar Aliyu Muhammad Gusau, ya ce Gwamna Matawalle ko wani wakilin jam’iyyar ba a samu wanda ya tuntube shi ba gabanin sauyin shekar.
Kazalika, ya ce ba shi da wata masaniya game da shirin Gwamna Matawalle na sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.
Sai dai ya ce tabbas ya ji rade-radi inda kuma ya samu gaskatuwar lamarin yayin da sauyin shekar da Gwamna Matawalle ya yi ya tabbata a ranar Talata.
A cewarsa, ya lura da gayya aka ki tuntubarsa domin jefa shi cikin tsaka mai wuya da zummar a samu tsamin dangartaka tsakaninsa da Gwamna Matawalle.
Ya bayyana sauyin shekar da Gwamna Matawalle ya yi a matsayin “wata babbar dama ta sake tumke damara domin tunkarar kalubalen da jama’armu ke fuskanta.
“Za mu samu nasarori da dama yayin da muka sabunta karsashinmu na fusktar duk wani kalubale,” a cewarsa.