✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina nan a Abuja, ban tafi Amurka ba – Tinubu

APC ta ce batun cewa Tinubu ya tafi Amurka don ganawa da Shugaba Biden sharrin mahassada ne kawai a fagen siyasa.

Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar APC, ya ce dan takararsu, Asiwaju Bola Tinubu, bai tafi ko’ina ba, yana nan a Abuja.

Kwamitin ya bayyana hakan ne domin karyata rade-radin da ake yi cewa Tinubu ya keta hazo zuwa Amurka don ganawa da Shugaba Joe Biden.

Kakakin kwamitin, Bayo Onanuga ne ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) hakan ranar Laraba a Abuja.

Ya ce labarin Tinubu ya tafi Amurka ba gaskiya ba ne, don haka ya ce jama’a su yi watsi da shi.

Ya kara da cewa, hoton Tinubu tare da Shugaba Biden da aka yada sharrin mahassada ne kawai a fagen siyasa.

(NAN)