Ga duk wanda ke bibiyar dambarwar siyasar kasar nan a kwanan nan, ba zai gaza jin yadda Shugaban Majalisar Dattijai da ke wakiltar Arewacin Jihar Yobe, Sanata Ahmad Lawan Ibrahim ke fuskantar babban kalubale ba, musamman game da kokarin da yake yi na dawowa majalisar a zaben 2023 da ke tafe.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Damaturu ce ta ce faufau ba shi ne halattaccen dan takarar Jam’iyya APC ba, hukuncin da ya hana shi tsayawa takara.
Wannan ne dalili da ya sa mutane ke tambayar ina makomar siyasar Sanata Ahmad Lawan?
Shin shugaban na da sauran tagomashi nan gaba a harkokin siyasa a matakin kasa da jiharsa ta Yobe, ko kuwa ruwa ya kare wa dan kada ke nan?
Sanata Lawan, dan siyasa ne da ake damawa da shi tun daga dawowar mulkin dimokuradiyya a 1998, inda a matsayinsa na tsohon malamin jami’a ya samu kansa a harkokin siyasa.
Ya fara sa kafarsa a zauren Majalisar Wakilai ya wakilci mazabarsa ta Bade da Jakusko a karkashin Jam’iyyar APP, daga 1999 zuwa 2007 – tsawon shekara 8.
Daga nan ne ya haye zuwa Majalisar Dattawa, a karkashin jam’iyyun ANPP, da APC. Haka kuma, a karkashin APC ce ya zama Shugaban Majalisar Dattawa.
Abin da masana suka hango
Masana harkokin siyasa na ganin matsalarsa ba za ta rasa nasaba da tsayawarsa neman takarar shugabancin kasa a zaben share-fage, inda da ya kasance daya daga cikin ’yan takara da suka fafata da Sanata Bola Ahmed Tinubu da ake ganin tamkar ubangidansa.
Sun yi hasashen cewa, watakila dalili ke nan da ake masa bi-tada-kulli tare da goya wa abokin takararsa, Bashir Machina baya, don ganin bayansa.
A wani bangare kuma wasu na ganin cewa shi kansa Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni ba ya tare da shi a siyasance, duk da cewa a fili kamar yana tare da shi, lura da yadda suke gudanar da harkokin siyasarsu tare.
To amma siyasa ta gaji rufa-rufa.
Na dauki lamarin a matsayin kaddara —Sanata Lawan
Aminiya ta tuntubi wani makusancin Sanata Ahmad Lawan a siyasance, Alhaji Usman Katuzu Gashuwa, kan abin da zai ce dangane da makomar siyasar Shugaban Majalisar Dattawan, bayan cikar wa’adinsa.
Sai ya ce, “Sanata Ahmad Lawan a siyasance babu wani tasgaro da zai samu ko kadan, ballantana a ce wai zai rasa wata makoma tagari dangane da siyasar kasar nan, domin kuwa lamarinsa akwai dattaku da sanin ya kamata tattare da shi, ta yadda duk wainar da za a toya dangane harkokin siyasa da mulkin kasar nan, na hakkake sai an dama da shi.”
Ya kara da cewa, a matsayin Ahmad Lawan na mutum mai biyayya da hangen nesa, lokacin da kotu ta ce ta dakatar da shi daga shiga takarar, cewa ya yi alhamdu lillah, ya rungumi kaddara, ba kuma zai daukaka kara ba a kashin kansa.
“Yadda ya yi addu’ar Allah Ya sa a gama lafiya tare da gode wa al’ummar mazabarsa kan goyon bayan da suke ba shi a kowane lokaci, ya nuna yana da kyakkyawar makoma a siyasance.
“Duk mai wannan hali ba abin jefarwa ba ne a duk wani abu da ya shafi al’umma.”
‘Babu wanda muke zargi a lamarin’
Kan ko suna zargin wani ko wasu dangane da koma-bayan da Sanatan ya samu a kudirinsa na sake komawa majalisar, sakamakon hukuncin da kotun ta yanke, sai Alhaji Usman ya ce, “Mu a matsayinmu na makusantansa, ba mu taba zargin kowa kan rashin nasararsa a kotu ba, illa mun san cewa duk yayin da wa’adin mutum ya kawo karshe a wani jagorancin da yake yi, to labudda da so da kin sa ba wani mahaluki da zai sa ko ya hana; domin lamari ne daga Allah.
“Don haka cewa da wasu ke yi wai ai rashin nasararsa na da nasaba da tsayawarsa takara da Bola Ahmed Tinubu ko wai Gwamna Buni ne ba ya tare da shi, duk zance ne kawai.
“Allah dai Shi ke ba da mulki ga wanda Ya so a lokacin da Ya ga dama. Mu dai a saninmu, a matsayinsa na mutum mai biyayya, yana da kyakkyawar dangantaka a tsakaninsa da Mai girma Gwamna Buni.
“Haka a sanina, ba ya da wani boyayyen lamari a tsakaninsa da dan takararmu na Shugaban Kasa a jam’iyyarmu ta APC, Sanata Ahmed Bola Tinubu, illa dai ’yan kai-kawo ne ke maganganunsu,” inji shi.
Za mu daukaka kara —APC
Aminiya ta yi ta kokarin jin ta bakin Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Yobe, Alhaji Muhammadu Gadaka game da labarin da ke yawo, cewa jam’iyyar a matakin jiha za ta daukaka kara amma lamarin ya ci tura, har zuwa hada rahoton nan.