✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina dandana gishiri ne!

Wani Bahadeje ne ya ba matarsa kaza domin ta dafa masa, amma ya ce mata kada ta ci ko kadan. Bayan ta gama dafawa ta…

Wani Bahadeje ne ya ba matarsa kaza domin ta dafa masa, amma ya ce mata kada ta ci ko kadan. Bayan ta gama dafawa ta sauke, sai ya dawo gidan amma matar ba ta kusa. Sai ya bude ya firgi cinya daya, ya shige ban-daki yana ci. Can sai ita ma ta zo ta bude tukunyar, sai ta fizgi cinya daya, ta shiga ban-daki da nufin ta cinye a boye, sai ta yi arba da mijinta yana cin nama, sai ta ce masa: “Da ma na kawo maka ne don ka hada ka cinye!” Shi kuma cikin kunya ya ce mata: “Ina dandanawa ne in ji ko gishiri ya ji.”
Daga S. Adamu, 08065635097