Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya bayyana kwarin gwiwarsa kan nadin Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau kuma shugaban Majalisar Sarakunan jihar.
Makarfi ya bayyana hakan ne a wata wasikar sakon taya murna da ya aikewa sabon sarkin ranar Laraba.
Ya ce, “Na yi amanna cewa sabon sarkin zai yi amfani da tarin basirarsa wajen samar da ingantaccen jagoranci ga masarautar Zazzau da ma Majalisar Sarakunan jihar a wannan lokacin mai cike da kalubale.
“Ina da kwarin gwiwar sarkin zai zama wata babbar rumfa da zata samar da inuwa ga dukkan Zage-zage har ma da wasu.
“Ina addu’ar Allah ya ba shi karfi, lafiya, juriya da kuma jajircewa wajen sauke wannan nauyin da aka dora masa. Allah kuma ya ci gaba da yi masa jagora da kariya,” inji Makarfi.
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Laraba ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya sanar da Ahmed Bamalli a matsayin sarkin Zazzau na 19, biyo bayan rasuwar tsohon sarki, Alhaji Shehu Idris a kwamankin baya.