✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina da burin zama gawurtacciyar ’yar siyasa a Najeriya – Hajia Talle Muhammad Hadejia

Hajia Talle Muhammad Hadejia wata fitatciyar ’yar siyasa ce da ta yi fice a yankin masarautar Hadejia da ma Jihar Kano, tun zamanin Malam Aminu…

Hajia Talle Muhammad HadejiaHajia Talle Muhammad Hadejia wata fitatciyar ’yar siyasa ce da ta yi fice a yankin masarautar Hadejia da ma Jihar Kano, tun zamanin Malam Aminu Kano; tana cikin jamiyar PRP, a lokacin ita ce mai bai wa Jam’iyyar PRP shawara afannin sharia wadda ake yi wa lakabi a Turance da “Legal Adibiser.”
A yanzu ita ce shugabar mata ta jam’iyyar PDP ta Jihar Jigawa a halin yanzu duk da tana siyasa bai hanata yin sana’a ba. Hajia Talle ta yi fice akan harkar saye da sayarwa, inda ta fara da sayar da atamfa a tsakanin ’yan siyasa mata, daga bisani da taga sana’ar babu wata riba, ta auna, sai ta yanke shawarar yin abincin sayarwa a Gurka kasuwar Jabo da kuma cikin garin Hadeja, wadda har gobe ana girkawa, ana saukewa da nufin dogaro da kai.
Hajia Talle ta samu nasarar fasa kurjinta da ya jima yana damunta, musamman akan yadda aure yake yawan mutuwa a kasar Hausa, da kuma yadda marayu suke fadawa cikin wani hali sakamakon rashin jin dadi da suka rasa na rashin mahaifansu. A hirar da ta yi da wkailin Aminiya, ta bayyana al’amura da dama. Ga kuma yadda hirar ta kasance:
Tarihinta
Ni hajia Talle Muhammed Hadeja, an haife ni a garin Kaugama, a wani kauye da ake kira Tauran Yamma, da ke cikin yankin masarautar Hadeja, kimanin shekaru 52 da suka gabata. Na tashi ban san mahaifiyata ba, domin sai da aka yi tiyata bayan rasuwar mahaifiyata aka cironi daga cikinta. Na zo duniya, na kuma girma a wajen kanwar mahaifiyata domin ita ce ta dauki  nauyin rainona a wani kauye da ake kira Tarabu da ke yankin karamar Hukumar Kirikasamma duk a masarautar Hadeja.

Daga  bisani aka yi mini aure, a lokacin da na kai minzalin aure, amma Allah bai sanya aurena ya dade ba;  na samu matsala da mijina auren ya fara tangal-tangal har ya mutu na koma gidan wani kanin mahaifina da ke zaune a Hadeja, inda na fara zawarci domin na sake yin aure .

Siyasa
Na shiga siyasa ne sakamakon ziyarar Malam Aminu Hadeja a lokacin zai fita yawan kanfen a zagayen masarautar Hadeja, sun fito kofar gidan danjani, sun jera motoci ana ta guda sai na fito kallo, sai wata mace ta ce ke fa ba za ki wajen taron ba? A lokacin za su tafi Guri ne, sai na ce za ni, sai suka ce min na shiga mota a lokacin da ma PRP tana da mata takwas kacal; shiga ta cikinsu sai muka zama mu tara. Da muka isa Guri bayan an yi laccoci, sai aka ce wa matan nan su yi magana, suka kasa, sai aka ce min ko zan yi, sai na ce zan yi; na tashi na yi wa mata lacca. Daga nan ne aka nada ni sakatariyar jam’iyyar
Daga wannan taron har Kano da Kaduna ana kirana idan za a yi taro na yi Jawabi. Sakamakon gogewa ta a fagen siyasa yasa jam’iyyar PRP, ta wancan zamani ta nadani Legal Adibiser har ta kai aka ba ni shugabar riko ta mata ta jam’iyyar. Saboda namijin kokarina a lokacin kuwa duk fadin Hadeja mata tara ne, wadanda muke yin PRP.
A lokacin siyasa ba irin ta yanzu da hauragiya da wawura da kyashi suka yi yawa a zukatan mutane, babu bakin ciki, babu maganar takardar shaidar karatu muddin kana da jama’a za ka iya tsayawa takara  kuma a zabeka. Idan  yanzu ne aka nadani mukamin da na rike a baya ina sabuwa aka ban mukami, sai na shiga gaba da wadanda na samu a ciki, amma su sun yarda na zama shugabarsu, ba tare da wani nuna kyashi ba. Domin ni kaina
ba na yin komai sai na yi shawara da su.
Iyali
Ina da ’ya’ya, amma ba zan fadi yawansu ba; saboda a al’adar mu da kunya  na bayyana yawan yayana. Domin fadar yawansu a wurina tamkar rashin kunya ne a wajena, ta yadda idan suka ganni a jarida za su ce na yi rashin kunya. Wannan yasa ba zan ce komai ba, a kan iyalina.
Batun aure
Ba ni da aure, kuma ina da burin yi, domin ban wuce yin aure ba, tunda har yanzu ban daina haihuwa ba. Kuma a rayuwata aure na biyu. Ina son dai in samu miji mai kyan hali, mai nagarta, wadda yasan me yake yi, wanda yasan rayuwa. Ba na san in auri mutumin da ba shi da tsari a rayuwarsa, domin duk wanda ba shi da tsari irin na addini bai san yadda zai tafiyar da rayuwar iyalinsa ba.