✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina da burin bude shago don inganta sana’ata -Abdullahi Wanzan

Wani matashi mai sana’ar wanzanci mai suna Abdullahi Nagwandu Wanzan da ke unguwar Idi’araba da ke karamar Hukumar Mushin a Jihar Legas, ya ce yana…

Wani matashi mai sana’ar wanzanci mai suna Abdullahi Nagwandu Wanzan da ke unguwar Idi’araba da ke karamar Hukumar Mushin a Jihar Legas, ya ce yana da burin bude shago, inda zai inganta sana’arsa ta askin zamani kuma yana fata nan ba da dadewa ba kalubalen da yake fuskanta ya kasance tarihi.
Abdullahi Wanzan, mai kimanin shekaru 26 ya yi furucin haka ne yayin da yake tattaunawa da Aminiya, a karshen makon da ya gabata.
“Kodayake al’amura a Jihar Legas, komai yana da tsada, babban kalubalena shi ne samun bude shagon da zan rika yi wa jama’a aski, amma ban cire ran cewa Allah zai cika min burina ba. Idan na bude shago zan samu jama’a, saboda an sami kebanta da natsuwa, maimakon a waje, inda ba kowa ke sha’awar ya zauna a yi masa aski ba. Idan Allah Ya hore min, zan sanya kayan aski iri-iri da sinadaransu na zamani da na gargajiya kala-kala. In kawata shagon, ta yadda kowa ya gani, zai sha’awarsa kuma ya yi burin dawowa gobe”. Inji shi.
Abdullahi, wanda dan asalin garin dundaye ne a Jihar Sakkwato, kuma yake da mata daya, ya ce ya gaji sana’ar wanzanci ne a wurin mahaifinsa, kuma ya  yi fiye da shekara 10 yana wanzanci tare da dogaro da ita a harkokin rayuwarsa, kodayake yakan hada da sayar da yajin nama ga mahauta.
Ya bayyana cewa a halin yanzu ba shi da burin canja wata sana’a, amma idan Allah Ya canja masa sana’a babu yadda zai yi.