Kocin kungiyar kwallon kafa ta mata da Najeriya da aka fi sani da Falcons Mista Edwin Okon ya yi ikirarin cewa kawo yanzu yana bin Hukumar NFF bashin albashin watanni 25 wanda ba ta biya shi ba.
Kocin ne dai ya horar da matan Najeriya da suka samu nasarar lashe gasar cin kofin Afirka ta mata da aka kammala a Namibiya a ranar Lahadin da ta gabata, inda Najeriya ta lashe kofin har sau bakwai. Ta samu nasarar lashe kofin na bakwai ne bayan ta lallasa Kamaru da ci 2-0 a wasan karshe.
Kocin, wanda shi yake horar da kungiyar kwallon kafa ta mata ta Riber Angels da ke Fatakwal ya bayyana takaicin ganin yadda Hukumar take masa rikon sakainar kashi na kin biyansa albashi da kuma wasu hakkokinsa duk da irin nasarorin da ya samu na horar da kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya (Falcons). Hasalima ya ce tun da suka halarci gasar cin kofin Afirka na mata a Nimibiya kawo yanzu ba a tura masa ko sisin kwabo a matsayin kudin alawus ko na albashi ba.
“Tun cikin watan Agustan 2012 a lokacin da na jagoranci kungiyar kwallon kafa ta Super Falcons a gasar cin kofin duniya inda muka samu nasarar zama na hudu kawo yanzu ban karbi ko sisin kwabo a matsayin albashina ba daga Hukumar NFF”, inji kocin a lokacin da yake hira da manema labarai.
“A duk lokacin da na kai kukana zuwa ofishin Hukumar NFF sukan shaida min cewa babu kudi, amma abin bakin ciki shi ne yadda nake samun labarin Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin a biya wasu daga cikin kococin da ke horar da kungiyar kwallon kafa ta kasa bangaren maza da suka hada da Stephen Keshi da sauransu amma ni an yi biris da ni”.