✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ina amfanin irin wannan rayuwar?

Gardama ce ta turnuke dangane da halin rayuwar da muke ciki, wasu na ganin cewa ai matsalar kuncin rayuwa a yau talaka ne ke jawo…

Gardama ce ta turnuke dangane da halin rayuwar da muke ciki, wasu na ganin cewa ai matsalar kuncin rayuwa a yau talaka ne ke jawo wa kansa saboda kwadayi da rashin godiyar Allah. Ban sa baki ba a cikin muharawar ganin cewa ba kowa ne ke da tsinkayar irin halin da muke ciki a yau ba. Saboda kuncin rayuwar wani ma na iya aza ka bisa matsayin da ba a kai kake ba, kana so ko ba ka so. Matsi ne ya sa na tofa albarkacin bakina, inda na tuna wa wadanda muke musun da su cewa shi mai tarin dukiya ai ba wanda ya fi shi laifi, domin kuwa dukiyar tasa a lokuta da dama ba ta da wani amfani, su kuma wadanda ke kan mulki ai yawancinsu makafi ne, ko kuma na ce summum-bukumum. Nan take sai wani ya ce ai mun san inda ka nufa, musamman da yake ba ka kaunar masu kudi ko mulki. Nan take sai na ga abin da na guda, amma na daure na ce ko a wannan ina da dalili ai. Na kwashe abin da na taba fada game da haka a can baya, na kare da cewa bai wai kdyama ba ce, ga dalili.

Ga wadanda ke ganin kamar na ki jinin masu tarin dukiya ta fitar hankali ko wadanda duk rayuwarsu ba abin da suka bige irin su hau dokin mulki, su yi sukuwa irin yadda suke so; ni tambayar da nake yi ita ce, ina amfanin tarin dukiyar ga wanda ya tara ta fitar hankali, yana kuma kwalliya da ita domin cin mutuncin wanda bai da ita ko yake fafutikar samun na kai wa bakin salati? Mu tsaya mu tambayi kanmu, mu yi wa kanmu hisabi. Shin mutumin da ya tara dukiya sama da Naira biliyan 1,980 shi kadai, sa’annan shekarunsa sama da 60 ko 70, me zai yi da wannan tarin dukiyar? Wace irin dadin rayuwa zai ji da wannan ‘kazamar dukiya,’ musamman idan aka dubi halin da wasu miliyoyin jama’a ke ciki; wasu ’yan uwansa ne, wasu makwabtansa ne, wasu ’yan garinsu ne? kila wani ya ce ina ruwana da wannan, ai dukiyarsa ce! Haka ne amma sai na sake tambayar, me zai yi da wannan tarin dukiyar shi kadai? Mu bi lissafin biliyan guda mu gani! Daga kididdigar da aka yi, idan mai biliyan guda zai zauna bai aikin komai a rayuwa, sai dai ya sa hannu karkashin matashi ya zaro dubu hamsin, ya kashe yadda ya so, zai yi shekara kusan 54 yana kashe dubu hamsin kullum, biliyan guda ba za ta kare ba, har ma zai samu rara! To don Allah ina ranar dukiyar wanda ya tara biliyan 1,980 shi kadai, alhali biliyan daya ma bai cinye ta a cikin shekara 55? Shekara nawa zai yi a rayuwa? Wa zai bar wa dukiyar? ’Ya’ya da jikoki? Su kuma shekara nawa za su yi a rayuwa? Shekara 100? Su nawa ne? Mu dauka ma su 100 ne ya haifa, biliyan daya ta ishe su, su ci har su mutu! To ina zai kai sauran bilyan dubu da 980? Ni sai na dauka akwai batan basira a tattare da wannan rayuwa ko tunani!
Ba wannan ke damuna ba kadai, akwai masu irin wannan tarin dukiyar ta fitar hankali a nan kusa da mu masu tarin yawa, idan ma ka ce biloniyoyi kake bida a Arewacin kasar nan, ba su lissafuwa, to ina amfanin wannan tarin dukiyar, alhali masu ita ba su cin abincin kwarai! Ba su barcin kwarai! Wasu ma sun kasa aure saboda neman abin duniya. Wasu sun yi auren sun hana matan haihuwa don kada su bata musu tsarin rayuwa! Wasu sun haifi ’ya’ya biyu, sun rufe mahaifar, wai kada yawan ’ya’ya ya sa su shagala da neman abin duniya! Ina amfanin wannan abin duniyar, bayan duniyar irin wadannan mutane ta dade da gigita? Ina amfanin irin wannan tarin dukiya alhali wasu na kusa da mai ita na fama da radadin talauci da yunwa da fatara?
Wannan ke nan! Amma wani abin da ya fi sa min takaici bai wuce yadda wasu shugabannin ko masu hannu-da-shuni ke bakanta wa talaka da marasa shi ba! Ina amfanin bukukuwan auren da wasu shugabanni ko masu hannu ke yi a rayuwa irin ta yau? Shugaba ne ko wani hamshaki zai aurar da ’ya’ya, musamman mata, duk bakin da suka je wajen taron biki ko walimar uwa ko ta kaka ko ta amaryar ko ta….Ga su nan dai, sai sun fito da ko dai akwatin talabijin filasma ko agoguna ko gwalalai ko wata kyautar alatu da in ka dididdige abin da aka kashe wajen sayen abubuwan kyautar alatun, sun ishi a gina rijiyar burtsatse 100 ga talakawan kauyukan da ke kusa da kauye ko gari ko birnin da wannan shugaba ko hamshaki ya fito! Ina amfanin irin wannan shugaba ko hamshaki a cikin al’umma, tun da hankalinsa ragagge ne? Ba ma wannan ba, shin an taba lura cewa kyaututtukan alatun da suke rabawa da abincin da ake ci a wurin walimar ba su da amfani ga wadanda aka ciyar ko aka ba kyaututtukan, domin su ma sun taka, sun karya? Sun sha, sun ci, sun gyagije! Ba talakawa ake ba kyaututtukan ba, abincin kuwa sai dai a zuba shara ko a ba karnuka, tun da ba cinyewa za a yi ba. Ina amfanin badi ba rai?
Mu dauka ma ai ana tara dukiyar ko neman mulkin saboda a bar wa magada, wato na baya, wai kada a bar ’ya’ya da jikoki cikin kunci da talauci, tambayar da nakan yi ita ce, shin su masu tarin dukiyar ta fitar hankali ko shugabannin da ke kan karagar mulki a yanzu suke ta wawura domin ajiye wa na baya, su wa ya tara ko ya ajiye musu? Nawa daga cikin wadanda suke hamshakai a yau iyayensu ko kakanni suke hamshakai a can baya? Me ya sa su ba su mutu ko sun sha wahala daga kunci da talaucin da iyaye ko kakanni suka gadar musu ba? Me ya sa su nasu idanun suka rufe, ba sa gane gaskiya, sai budun-buduma? Shin tambayar da nakan yi ita ce ina amfanin dukiyar da za a bar wa magada wadda ba ta ceto ko taimakon wanda ke da ita ko wanda ke kusa da shi? Mu tuna fa idan tarin dukiya shi ne dadin rayuwa, ina karuna? Idan mulki da isa shi ne abin tokabo, ina Fir’auna? Wannan ita ce amsata ga masu musayar ra’ayin da muka yi, ko a yarda ko kada a yarda!