✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ina alfahari da tsare ni a kurkuku duk da ban aikata lafi ba —Jarumin Nollywood

Fitaccen jarumin masan’antar shirya fina-finan Kudancin Najeriya (Nollywood) Moses Armstrong, ya ce ya yi  farin ciki da aka tsare shi a gidan yari, duk da…

Fitaccen jarumin masan’antar shirya fina-finan Kudancin Najeriya (Nollywood) Moses Armstrong, ya ce ya yi  farin ciki da aka tsare shi a gidan yari, duk da cewa bai aikata laifin fyaden da ake zargin sa ba.

Jarumin da aka gurfanar da a gaban kotun Oyu, ana zargin sa ne da aikata laifin fyade, da hadin baki, hadi da ba da magungunann zubar da ciki, sai dai ya musanta zargin.

Jarumin ta shafinsa na Facebook ya ce dalilinsa na wannan furuci shi ne, yadda ya fi jin kusancinsa da ubangijinsa a zamansa a gidan gyaran halin.

Ya kuma ce yana da labarin da zai bai wa masu bibiyarsa ta shafukansa na sada zumunta, kan abubuwan birgewa da ya gani a zamansa a gidan yarin.

Kotun Jihar Akwa Ibom ce dai ke sauraren shari’ar ta Armstrong da gwamnatin jihar, kuma ta sanya an tsare shi ne tun ranar 13 ga wanan Yuni.

A karshe dai kotun ta bada belinsa kan Naira miliyan biyar.