✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

In Za Ka Fadi… Arewa: Shekau a rigar Turji…

Kullum Arewa ta zama ita ce makwantar rikici rigingimu da masifu iri-iri daga an fita wannan sai a fada wancan.

Babu ko tantama wannan tashin-tashina da ake fama da ita a Arewa aba ce da aka zauna aka kitsa ta da nufin wargaza mu.

Eh, haka ne, in ba haka ba, me ya sa tashin hankali daga wannan sai wancan?

Kullum Arewa ta zama ita ce makwantar rikici rigingimu da masifu iri-iri daga an fita wannan sai a fada wancan.

Ana murna an gama da Shekau, ana ganin kamar hakan zai kawo saukin fitinar Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas musamman a jihohin Borno da Yobe, ana murna mutane sun fara komawa garuruwansu da suka yi wa kaura shekaru da dama su yi noma su yi kasuwanci su gyara gidajensu da suka zama kufai domin fara wata sabuwar rayuwa.

Abubakar Shekau da Abu Mus’ab Albarnawi wadanda su ne jagororin Boko Haram da suka hana al’umma zaman lafiya, suka jagoranci kisan dubban mutane, suka barnata dukiyoyin da Allah ne Ya san yawansu, suka mayar da mutane ’yan gudun hijira a jihohinsu, suka mayar da mutane almajirai suna neman abin da za su ci su rayu, suka sanya wa mutane bakin ciki da damuwa marar misaltuwa.

Mata da yawa suka zama zawarawa sakamakon kashe mazansu, yara da dama aka mayar da su marayu karfi da yaji aka sanya musu tsoro da zullumi.

Aka jefa wa sauran mutanen Arewa tsoron duk wani mutumin yankin Borno.

Da an ga bakon fuska da zane a fuskarsa irin na Barebari ko yana Hausa irin tasu sai ka ga ana tsoron sa ko ana kaffa-kaffa da shi, duk mutanen yankin da Boko Haram ta ragargaza kallon da ake yi musu ke nan, sun sani ko ba su sani ba.

Irin masifar da su Shekau suka jefa al’ummar wannan yanki Allah ne kadai Ya san ta, sun cutar da garuruwansu da al’ummarsu, sun sanya an kyamace su a lokacin da suke tsakanin neman taimako.

Abin da Shekau da Albarnawi suka jawo wa mutanen jihohin Borno da Yobe Allah ne kadai ya san irin illlar da suka yi.

Har aka kashe su, suna wulakantattu ba su ci nasara ba, sai dai hasara da suka yi da kuma wadda suka jefa mutane a cikinta.

Duk abin da Shekau da Albarnawi da masu bin su suke ikirari sun ji kunya a kansa, babu abu guda da suka ci nasara a kai, Musulmi suna nan suna Sallah ba su fasa ba, Kiristoci suna nan suna addininsu ba su fasa ba.

Haka kurum Shekau ya tashi ya jefa al’umma a cikin masifa da sunan wai suna yin addini ba daidai ba.

Ranar Alkiyama idan Allah Ya tambayi Shekau mutum nawa ya hallaka ko ya sa aka hallaka shi kansa bai sani ba, amm Allah Ya sani.

Yaya zai yi da jinanen al’ummar da ya hallaka ba su ji ba, ba su gani ba?

Wata shari’a sai Allah kurum, amma duk yadda mutum ya so ya wassafa ta sai ya gaza yadda zai suranta abin.

Muna murna za mu yi ban kwana da Boko Haram sakamakon kashe Shekau, amma sai abu ya ki ci yaki cinyewa.

Shekau din da muke burin a kashe an kashe shi tabbas, amma yana nan ya sake bulla da wata sabuwar riga ful da wani sabon suna ful shi ne Bello Turji.

Wannan dan taliki da ya waiwayo yankin Arewa maso Yamma yana ta’addanci da kashe mutane da jefa tsoro da firgici da zullumi a tsakanin al’umma musamman matafiya, tamkar Shekau yake.

Me yake so? Me yake nema? Laifin me aka yi masa? Su wa suka yi masa laifin?

A makon jiya al’ummar Najeriya suka wayi gari da mummunan labarin kisan wadansu matafiya mutum 23 a Karamar Hukumar Sabon Birni, inda aka cinna wa wadannan bayin Allah wuta a cikin mota suka kone kurmus.

Kallon hoton abin da ya faru kadai ya isa tashin hankali! Balle kuma wanda suka ga abin ko suka fara zuwa kan gawarwakin wadannan bayin Allah.

Yanzu don Allah da Bello Turji da jama’arsa wane dadi suka ji da wannan mummunan aiki na ta’addanci da suka yi?

Shin sun samu natsuwar zuciya da kisan wadannan bayin Allah? Laifin me matafiyan suka yi musu?

Wato wannan shi zai nuna maka Bello Turji da jama’arsa ba su san Allah ba, kuma ba za su taba jin wani roko ko magiya ba.

Don haka batun sulhu da su ma bata lokaci ne, duk mutumin da bai san Allah ba, ai ba ya so gaskiya ba.

Bai kuma san laifin karya alkawari da cin amana ba, to, irin wadannan mutanen da ba su san Allah ba, wace yarjejeniya za a kulla da su a samu zaman lafiya?

A dauri kashi ko a bata igiya? Ni na gamsu yin sulhu da su ba ya da wata fa’ida, domin ba su san Allah ba, kuma ba su san alkawari abin tambaya ba ne a wajen Allah.

Duk mutumin da bai san wannan ba, ai babu wata fa’ida ka yi wata yarjejeniya da shi.

Yaren da suke magana da shi, shi ne kawai za a yi musu magama da shi.

Duk wata kofa ta tattaunawa don samun zaman lafiya wadannan mutanen sun sa mukulli sun rufe ta, to bai kamata har yanzu a samu masu tunanin a yi sulhu da wadannan mutane ba. A bi musu ta yadda suke so.

Abin da kawai ya rage shi ne gwamnati ta fuskanci abin da gaskiya kuma don son kasa da al’ummar kasa, a bi mutanen nan duk inda suke a far musu.

Duk yawan jami’an tsaron kasar nan da manya da kananan sojoji da horon soji da ake tura jami’an tsaro su je Birtaniya da Indiya da Isra’ila da Amurka duk yana suna?

Ina jiragen yaki? Ina sababbin jiragen Tucano da aka sayo? Yanzu ne ya kamata a yi aiki tsakani da Allah a sa kishin kasa da al’ummar kasa.

Muna da sojojin ruwa da na sama da na kasa, suna ina? Aikin me suke yi? Ina ’yan sanda? Wallahi Turji bai gagari hukuma ba, an san inda yake, an san hanyoyi dubu da za a iya bi a kama shi da hannu ba tare da bindiga ba.

A nan ya kamata hukumomi su ji tsoron Allah su sani Allah zai tambaye su a kan rayukan al’umma da suke salwanta.

A ceci rayuwar al’umma musamman wadanda suke yankunan Isa da Gwaronyo da Sabon Birni da Shinkafi a jihohin Sakkwato da Zamfara.

Bai kamata a zuba ido rayukan mutane suna salwanta haka kurum babu wani mataki da ake dauka na kokarin kawo karshen abu ba. Allah fa Yana kishin bayinSa.

Muna fata daga wannan lokaci shugabanni na dukkan bangarorin jami’an tsaro da suke da alhakin kula da rayuwa da dukiyoyin al’umma da Shugaban Kasa wanda dukkan wadannan abubuwan suka rataya a wuyansa, za su zage dantse a wannan dan lokacin da ya rage masa, su cire tsoro su yi abin da ya dace.

Ba ma fata a sake jin irin wannan mummunan labari da ya faru a Sabon Birni.

Muna fata duk inda wannan mujirimi Turji yake a bi shi a kashe shi a kubutar da mutanen da yake tsare da su.

Allah Ya ba mu lafiya da zaman lafiya, Allah Ya tona asirin Turji da duk masu mara masa baya.

Allah Ka ba mu lafiya da zaman lafiya.