✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Imo: Kotu ta daure tsohon Kwamishinan Okorocha shekara 3

Kotun ta sami tsohon Kwamishinan na Sufuri da laifin karkatar da N180m

Wata kotu a Jihar Imo ta yanke wa tsohon Kwamishinan Sufuri a zamanin da Rochas Okorocha yake Gwamnan Jihar, Lasbery Okafor-Anyanwu hukuncin daurin shekara uku a gidan gyaran hali.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan ta same shi da laifi a tuhume-tuhumen da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta yi masa.

Alkalin kotun, Mai Shari’a K. A Lewanya, ya ce an same shi da laifin damfara da karkatar da kudaden gwamnati da kuma sata.

An dai zargi tsohon Kwamishinan da laifin karkatar da kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan 180 ne zuwa asusun kamfanin da ya mallaka, lokacin da kuma shi ne yake rike da mukamin mai kula da kamfanin sufuri na Jihar (ITC).

Laifin a cewar EFCC, ya saba wa tanade-tanaden sassa na 12 da 19 na kundin ICPC na shekara ta 2020.

Alkalin ya kuma ce lauyan EFCC, Michael Ani, ya gamsar da kotun cewa Anyanwu ya karkatar da kudaden zuwa asusun ajiyar kamfaninsa mai suna Oma Oil ta haramtacciyar hanya.

Kazalika, kotun ta same shi da laifin batar da wata Naira miliyan 80, ita ma daga lalitar gwamnati zuwa kamfaninsa, da niyyar cewa zai sayo wasu motoci ne ga kamfanin na ITC.

Daga karshe dai kotun ta umarce shi da ya dawo da jimlar kudin har Naira miliyan 180 da ke asusun ajiyarsa zuwa kamfanin na gwamnati.