✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Illolin rashin barci ga rayuwar dan Adam

Rashin barci dai na haifar da cututtuka iri-iri, cikinsu har da kansa

Barci wani muhimmin abu ne da dan adam ke yi bayan ya yi aiki ya gaji.

Bacci yana ba wa jikin dan Adam da kwakwalwarsa hutu na wani lokaci, kamar yadda Dokta Ibrahim Musa, wanda likita ne a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano ya bayyana.

A cewar likitan, masana lafiya sun bayyana cewa yana da kyau matuka mutum ya sami bacci akalla na tsawon sa’a takwas a kullum wanda kuma hakan yana da tasiri sosai ga lafiyar jikinsa.

Dokta Ibrahim Musa ya jero amfanin bacci ga lafiyar dan adam kamar haka:

1. Bacci yana ba wa kwakwalwar dan Adam hutu yadda za ta iya yin wasu ayyyuka. Idan aka yi rashin sa’a mutum ba ya samun isasshen barci, to kwakwalwarsa za ta cunkushe da abubuwa da yawa.

2. Bacci yana ba dan Adam damar mayar da hankali kan abin da yake gabansa.
Haka kuma bacci yana kare mutum daga kananan hadarurruka. Misali matar da ba ta yi barci ba to akwai yiwuwar idan ta je yin girki to za ta iya yankewa a hannu saboda baccin da yake kanta wanda ba ta samu yin sa ba. Ko kuma direban da ke tuka mota zai iya yin hatsari idan bai samu yin barci ba.

3. Haka kuma rashin barci yana sa mutum ya rika yin wata irin kiba maras dalili.

4. Rashin samun isasshen barci yana iya haifar da ciwon zuciya.

5. Haka kuma, idan mutum ba ya samun isasshen barci to akwai yiwuwar kamuwa da cutar kansa.

6. Rashin barci yana sa garkuwar jikin dan Adam ta yi raumi yadda kowacce irin cuta ta zo jikinsa sai ta samu wurin zama.

Aminiya ta tattauna da wata mata da cutar rashin bacci ta kama mai suna Zainab Sani, inda ta bayyana cewa ta sha fama da ciwon kai mai tsanani wanda a karshe sai da takai ta da kwanciya a asibiti.