✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Illar bangar siyasa ga al’ummar Najeriya

An gano cewa ’yan bangar siyasa ne suka rikide suka zama ’yan Boko Haram.

Bangar siyasa dai ta zama kadangaren bakin tulu a Najeriya, kamar kuma yadda ta zama alakakai, mai jaza wa al’umma jamhuru kala-kala.

Ganin irin illar da ke tattare da al’amarin, Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa Katsina, Babban Sakataren Kungiyar Muryar Talaka ta kasa kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya yi dogon nazari game da ita.

Babban dan siyasa, marigayi Waziri Ibrahim ya taba furta wani kalami da ya zama tamkar tambari a siyasar Najeriya. Wannan kalami shi ne, “Siyasa Ba Da Gaba Ba.”

Marigayi Waziri na da tarihin sauya sheka, daga wannan jam’iyya zuwa waccan.

A irin wannan sauya sheka, ya taba barin jam’iyyar Dokta Nnamdi Azikiwe (Zik) ta NPP ya kafa GNPP a Jamhuriya ta Biyu, bisa dalilinsa na cewa yana son ya zama dan takarar Shugaban Kasa.

Irin wannan canje-canjen sheka tsohon al’amari ne da ya dade a siyasar Najeriya.

Kuma lallai wannan abin da ke faruwa a fagen siyasar Najeriya, yana nuna yadda ’yan siyasa suka dauki talakawa wawaye, gasorogo-in-ba-bawo.

Kwanakin baya na ji da kunnena wani dan siyasa na fadin cewa, wai aikin matasa shi ne su lika hotunan ’yan siyasa.

Abubuwan da ke faruwa fagen siyasar Najeriya, musamman na sauya sheka, bisa dalilai na son zuciya na kara fitowa fili, da cewa za a dauki lokaci mai tsawo ba a samu wani kyakkyawan sauyi a kasar nan ba.

Wadannan mutane babu ruwansu da halin da talaka yake ciki, burinsu su ci zabe ko ta halin kaka.

Su yi amfani da matasa domin a tada zaune tsaye, a yi banga a ci zarafin jama’a.

Wannan ya sa ko matasan Najeriya za su sauya hali? Ko za su gane cewa yaudarar su kawai ake domin su tura mota in ta tashi, ta bude su da kura, ta bar su a banza?

Lokaci na kara kurewa amma ’yan siyasa na ci gaba da amfani da matasa, suna mayar da su ’yan bangar siyasa, suna ba su kayan maye domin cin ma burinsu na siyasa.

Babu shakka lokaci ya yi da matasan ya kamata su ankara, su yi wa kansu kiyamul laili. Lokaci ya yi da za su mutunta kansu, su kaurace wa ayyukan daba, domin biyan bukatar wasu ’yan siyasa.

Sakamakon bangar siyasa, yau ga halin da kasarmu ta shiga. Hatta Boko Haram ta samu gindin zama saboda bangar siyasa, domin a Maiduguri da Bauchi da Gombe da Yobe, an gano cewa ’yan bangar siyasa ne suka rikide suka zama ’yan Boko Haram.

Dama ’yan bangar siyasa, mafi akasarinsu ba su samu damar samun ilimin zamani ba, don haka suna cike da fushin jama’a, don haka suke amfani da duk wata dama don huce haushinsu.

Bangar siyasa ta sa rubabbun ’yan siyasa na darewa madafin iko, in sun hau ba su daukar kowa da gashin arziki, sai dan bangar siyasa.

Akwai dan siyasar da ya shaida min cewa siyasar Najeriya ba ta ’yan boko ba ce, ta ’yan rashin da’a ce, wadanda za su zagi kowa, su ci mutuncin kowa.

Tambaya a nan ita ce, ta yaya za a kawo karshen wannan annobar?

To dama dai al’umma ta fi kowa cutuwa daga ’yan bangar siyasa. In ba su kashe ba, to sun hana kwana, inji wani mawaki. Al’umma kar su zabi duk dan siyasar da ke mu’amala da ’yan banga.

Game da halin rashin tsaro da Najeriya ke fama da shi a yanzu haka, masu iya magana na cewa tun ran gini ran zane.

Tun tuni, tun kafin lokaci ya kure masana da kwararru ke wa al’ummar Najeriya hannunka mai sanda, cewa abu kaza kan haddasa kaza, abu kaza kan haddasa mummunan sakamako amma shugabannin da sauran talakawa ba su damu ba.

Kullum sai korafi, ba a iya daukar kwakkwaran mataki. To yau ga halin da kasar ta shiga, inda kowa ke dandana kudarsa. To sai dai duk yadda al’ammura ke kara kazancewa a Najeriya, har yanzu wasu wai ne a wurinsu.

Akwai mutanen da idan dai ba su abu ya rutsa da su ba, to su babu ruwansu. Wannan tunani shi ya sa har yanzu ake samun masu karbar kudi wajen ’yan siyasa.

Wannan ya sa har yanzu da yawa mutane ba su iya wani abu don sadaukarwa. Abin ya tsaya a fatar baki da surutu kawai.

Wannan ya sa wasu ke ganin har yanzu da sauran rina a kaba, domin mutanen Najeriya ne kawai za su iya fitar da kansu daga halin da suke ciki ba wani ba.

Amma dan Najeriya ba zai fita daga halin ukubar da yake ciki ba, sai ya cire kabilanci, kiyayyar addini, bangaranci, hassada, bakin ciki, munafinci, annamimanci; sannan ne zai fara daukar hanyar fidda kansa daga cikin tsaka mai wuyar da yake ciki.

Wasu na batun wai a raba kasar. Ina ganin a halin da ake ciki, raba Najeriya bai da wani tasiri, illa ya kara jefa kasar cikin fitina.

Don haka batun raba kasa ba zai magance yunwa, fatara, bakin ciki, hassada, gaba, rowa, algungumanci da sauran halayen ’yan Najeriya ba.

’Yan Najeriya su dai kara dubawa domin samo mafita amma ba wai raba kasa da rura wutar kabilanci da addini ba.