Da ganin Iliyasu Ligale, dan kimanin shekaru 30 a duniya, ka san akwai karfi a tare da shi. Ba sai an gaya maka ba, da ka ga tsayinsa da irin kirar jikinsa babu shakka za ka yanke hukuncin cewa da wuya dan kokawa ya kayar da shi cikin sauki. Aminiya ta samu tattaunawa da shi kan irin gwagwarmayar da ya sha da kuma sirrin da ya sa ya gagari ’yan kokawa a Legas:
Abubakar Haruna, Daga Legas
Aminiya: Za mu so ka gabatar da kanka?
Ni sunana Iliyasu Ligale. Ni dan asalin jihar Tawa ne a kasar Nijer. Yau shekarata 30 a duniya. Na yi kusan dukkan rayuwata a Nijar, sai dai daga bisani na zo Najeriya don neman kudi.
Aminiya: Ya aka yi ka shiga kokawa?
Ni dai tun ina karami nake sha’awar kokawa. Saboda a kasarmu Nijar kokawa ita ce wasan da ya fi kowane wasan gargajiya fice. Akan je kallon kokawa da ni tun ina karami, ina ganin yadda ’yan kokawar Nijer da sauran kasashe suke yin kokawa da kuma irin dabarun da suke amfani da su a kan abokan hamaiyyyarsu. Tun daga nan sai na tashi da sha’awar abin a zuciyata. Tun muna yin kokawa irin ta yara har muka fara shiga ta matasa. Na fara tun daga kokawar unguwa har zuwa kauye har zuwa gari har na rika shiga kokawar kasa baki daya wacce ake yi mata lakabi da kokawar takobi.
Aminiya: Ashe ka taba shiga kokawar takobi?
kwarai kuwa na taba shiga kokawar takobi kuma na kayar da mutane da yawa. Na yi kokawa da fitattun ’yan kokawa daban-daban manya da kanana kuma na samu nasara a kansu.
Aminiya: Me ya sa ’yan kokawar Najeriya suke tsoron karawa da kai?
Ba komai ya sa ’yan kokawar Najeriya suke shakkar karawa da ni ba sai don sun san idan muka yi kokawa zan kayar da su. Har yau ba a taba samun wanda ya kayar da ni a nan Jihar Legas da kuma a Najeriya kakaf ba, babu dan kokawar da ya taba kayar da ni. Na yi kokawa a wurare da dama kamar jihar Legas da Fatakwal da Benin da sauran wurare da dama. Duk lokacin da na zo Najeriya har na koma ba a kayar da ni a kokawa sai dai na kayar har ya zama ma idan na je wadansu gidajen kokawar ba a tara ta saboda ’yan kokawa sun san zan kayar da su. Wani lokaci haka zan zo Najeriya amma sai na rasa wanda zan yi kokawa da shi.
Aminiya: Za ka iya lissafa mana fitattun ’yan kokawa da ka kayar a Najeriya?
Ba zan iya tuna sunayensu ba amma na san na je gidajen wasan kokawa da yawa a Najeriya na yi kokawa kuma duk wanda muka yi da shi sai na kayar da shi ka je ka tambayi masu gidajen kokawa a nan Legas.
Aminiya: Akwai wani dan kokawa da ya gagara a Legas ana yi masa lakabi da dan Ibo, ka taba kayar da shi?
Ba zan iya tunawa ba amma in dai yana kokawa a Legas babu shakka mun taba karawa kuma na kayar da shi. Akwai ‘yan kokawa da ba Hausawa ba da na yi kokawa da su kuma na kayar da su. Duk cikinsu babu wanda ya taba kayar da ni. Ka san ba na iya rike sunayenku na ’yan Najeriya amma kai da kanka ka ga lokacin da na zo gidan kokawa na Malam Sanda da ke Mil 12, mutane suna tsoron tara ta sai da aka yi mintina ina kirari amma an rasa wanda zai tare ni sai daga bisani Shagon Taliya ya yi ta maza don kada su ji kunya ya tare ni, shi ma ka ga kayin da na yi masa cikin dan lokaci kadan. Ba na ji kana kai da kanka kana cewa kana mamakin yadda suke tsorona ba? Ai ina jin ka, dole su ji tsorona mana saboda kwarewar ba daya ba ce.
Aminiya: Shin kana yin amfani da wani sihiri ne da yake sanyawa kake samun nasara a kan duk dan kokawar da ka hadu da shi?
Gaskiya ba na amfani da wani sihiri, ba komai a jikina in ba wannan layar da na rataya ba. Ita ma ba layar kokawa ba ce, ba ta da alaka da kokawar da nake yi. Ita kokawa tana bukatar kwarewa ne. Za ka ga wani ya fi ka karfi amma sai ka kayar da shi. Kodayake idan kwarewa da karfi suka hadu a wuri daya to babu shakka an samu abinda ake so. Za ka ga dan kokawar da ya hada wadannan abubuwa biyu ya gagara.
Aminiya: Wane dan kokawa ne ya fi tayar maka da hankali?
Duk dan kokawar da yake da naci da rashin tsoro ya fi daga mini hankali amma idan dan kokawa ya kasance matsoraci kuma rago to wannan ba na sanya shi a lissafi. Shi marar tsoro da ka shigo fili zai tare ka ba tare da tunanin abin da ka iya biyo baya ba. Haka ma mai naci wanda za ka yi kayar yau ka kayar gobe amma ba zai daina tarar ka ba to wannan yana burge ni. Don in dai kuna bugawa, to wata rana zai samu nasara a kanka.
Aminiya: Shin kana nufin wata rana za a iya samun wanda zai kayar da kai?
Ba na fatan hakan amma duk gwani ya san wata rana sai an samu wanda zai yi nasara a kansa. Kowa da lokacinsa. Idan ka hadu da wanda lokacinsa ne komai kwarewarka da dabararka sai ya yi nasara a kanka. Haka duniya take.