Ilimi gishirin zaman duniya. Idan babu ilimi, babu rayuwa mai kyau. Kamar yadda aka sani a Musulunci, ilimi wajibi ne ga namiji ko mace. Mace kamar namiji, akwai bukatar ta yi ilimi domin ita uwa ce, ita ke renon ’ya’ya, kuma halaye da dabi’unta abubuwan kwaikwayo ne ga ’ya’yanta.
A lokutan baya, ba a ba mata damar neman ilimi sosai ba, hasali ma, ilimi ba a damu a ba su iliminn addini ballantana na zamani. Har ana cewa “Sabbi saukar Mata”. Watau da sun kai Suratul Sabbi shi ke nan sun bar karatu da neman ilimi. Suratul Sabbi kuwa ita ce Surah ta 97 a Alkur ‘ani, kuma ita ce Izifi na daya daga cikin Izifi Shittin na Alkur’ani.
Mace a wancan zamanin, idan ta kai shekara 14 ko 15 sai a yi mata aure. Hakan yana da kyau kamar yadda addinin ya nuna. Yin aure bai kamata ya hana ilimin mata ba. Abin takaicin sai a bar su a gida ba su san yadda ake tsarki ba.
Daga baya da ilimin boko ya fara shigowa kasashen Hausa, sai aka dauki karatun Boko a matsayin wani abu marar amfani. Ba a ba ’ya’ya maza da mata damar su yi karatun ba. Bayan an fara gane muhimmancin karatun boko ne, aka fara ba maza damar yin karatun sosai.
A manyan makarantun boko akwai sashi daban-daban, wadanda dalibi zai iya yin karatu. Akwai kamar Likitanci da karatun zama Injiniya da na harsuna irinsu Turanci da sauransu. A bangaren karatun likitanci da Unguwarzoma, wadannan sashi ne da mata za su fi mayar da hankali, domin hakan zai amfani al’umma. A wasu asibitocin, maza ne wadanda ba muharramai ba ke duba mata. To a maimakon haka, zai fi kyau a ce mace ta duba ’yar uwarta.
Mafi yawancin tsokacin mutane a kan karatun ’ya’ya mata a kan yanayin makarantun ne. Yadda ake hada maza da mata, yadda tsarin sanya tufafi yake da sauransu. Idan har gwamnati na so ta habaka ilimin mata a Najeriya, musamman a arewa, ya zama dole ta yi la’akari da halayya da addini da zamantakewa da kuma al’adun mutune wajen tsara makarantu da kuma yadda ake karatun, haka zai taimaka sosai wajen bunkasa ilimi sosai a Arewacin Najeriya.
Ina so mata su sani neman ilimi wajibi ne, sai dai su sani ya zama dole su tsare kansu daga aikata dukkan ayyuka marasa kyawu, iyaye su sanya idanu wajen lura da yadda ’ya’yansu mata suke karatu.
Kwamared Abdulbaki Aliyu Jari
dalibi a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato.
Za a iya samunsa a wannan lambar +2348035424321