✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ilimi da jarabawar kammala sakandare sun zama kyauta a Kogi —Bello

Gwamnatin jihar za ta biya wa dalibanta kudin jarawar WAEC, NECO da JAMB

Gwamnatin Kogi ta sanar da shirinta na ba da ilimi kyauta ga dalibanta har su kammala makarantar sakandare. 

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana cewas shirin ilimi kyautan ”ya shafi daukacin dalibai ’yan asalin jihar, kuma ya kunshi biya musu kudaden jarabawar WAEC da NECO da JAMB gaba daya.”

Yahaya Bello ya sanar da haka ne a taron kaddamar da rabon kayan tallafi na Naira biliyan biyu da Gwamnatin Tarayyar ta samar domin raba wa al’ummar jihar.

Ya bayyana cewa rabon tallafin bai tsaya ga kayan abinci kawai ba, har da kudade da Gwamnatin Tarayya ta bayar a raba wa al’ummar jihar domin rage musu radadin cire tallafin mai.

A cewarsa, kayan tallafin zai su kai ga kowane rukuni na al’ummar jihar, ta yadda kowane gida zai samu, ba tare da la’akari da bambancin siyasa, kabila ko addini ba.

Shi ya sa gwamnati ta tsara rabon ta yadda za a yi a matakai daban-daban domin kayan su isa ga wadanda ya kamata.

“Kuna sane da cewa kananan hukumomi sun riga sun fara rabon kayan tallafin, wanna da muke yi kuma kari ne a kan kokarin da ake yi na rage wa al’umma radadin wannan tsari.

Yahaya Bello ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinun bisa tallafin da ya bayar domin rage wa al’umma radadin cire tallafin mai.

Aminiya ta ruwaito cewa duk da cewa a ranar da Tinubu ya karbi mulki ya sanar cewa biyan tallafin mai da ke lakume wa gwamnati tiriliyoyin Naira, ya zama tirihi; a watan Agusta, gwamnatinsa ta kashe Naira biliyan 169.4 wajen biyan tallafin.

Wasu masana dai sun bayyana cewa dawo da tallafin ya zama babu makawa, ganin yadda farashin litar fetur ya jima a kan N620 a Najeriya duk da cewa farashinsa ya tashi a kasuwar duniya.

Sun bayyana cewa da alama gwamnatin Najeriya ce ke biyan dillalan mai tallafi domin kada farashin ya haura N620 din.

Cire tallafin mai da gwamnatin Tinubu ta sanar ya sha suka daga kusan kowan bangaren al’ummar Najeriya, ganin cewa cikin dan kankanin lokaci farashin ya ninninku daga N195 zuwa N620, ga kuma wahalar samu.

Hakan ne ya haifar da tsadar kayayyaki wanda ya haifar da Allah wadai da al’ummar kasar da kuma zanga-zanga hadi da yakin aikin kungiyar kwadago, da nufin ganin gwamnati ta janye shi, ko kuma ta kara wa ma’aikata mafi karancin albashi daidai da yanayin tsadar rayuwa da ake fama da ita. Sai dai har yanzu kahar kungiyar ba ta cim-ma ruwa ba.

A kwanakin baya ma an yi ta rade-radin shirin karin farashin man, kafin daga bisani gwamnatin ta karyata.

%d bloggers like this: