Za mu so mu ji suna da kuma takaitaccen tarihinki.
Sunana Murjanatu Sulaiman Shika, ni ‘yar Shika ce a Zariya da ke Jihar Kaduna. Na yi makarantar firamare da sakandare a makarantar Unity School a Zangon Shanu da ke Samaru. Bayan na gama ne kuma na tafi Jami’ar Ahmadu Bello inda na karanci harshen turanci a digirin farko, sannan na sake yin digiri na biyu a wannan fannin. Bayan na kammala ne kuma aka ba ni aikin koyarwa a sashen koyar da harshen turanci na jami’ar ta Ahmadu Bello. A halin yanzu na yi aure, ina da ‘ya‘ya uku. Haka kuma ni ‘yar rajin kare hakkin bil’adama ce, musamman fannin da suka shafi yara da mata, inda nake shugabantar wata cibiyar taimaka wa al’umma musamman mata.
Masu karatu za su so su ji suna da ayyukan cibiyar da kike shugabanta?
Sunan cibiyar ‘Women Connect Intiatibe’, kuma ayyukanmu duka a kan mata ne, da kuma ‘ya‘ya mata. Mun fi mayar da hankali a kan lamurran da suka shafi matan, ta yadda za a taimakawa juna, da ci gabanmu gaba daya. Duk inda muka samu labarin mace da ke da kokari amma ta gaza samun wanda zai tallafa mata, mukan je mu kai tallafi. Mukan shiga sako-sako mu kai tallafi. Irin wannan ba wai yana nufin ka je kauyuka ka fito da mace ba, a’a a wurin da take za ka tallafa mata da abin da zai yiwu ta yi sana’a, don ta samu ta ci gaba. Wasu za ka ga suyar kosai ne, wasu dinki ne, da sauransu. Saboda haka mukan yi la’akari ne da abubuwan da mace ta fi iyawa, sai mu tallafa mata a kai, wasu ma ba sai sun fita daga gidajensu ba, a cikin gida suke gabatar da sana’o’insu, suna taimakawa ‘ya‘ya da mazajensu. Sannan su kuma ‘ya‘ya mata muna tallafa musu ne akan karatu, don kuwa duk macen da ka ba ta ilimi ka gama mata komai. Saboda komai kankantarsa da shi za ta yi amfani ta koya ma ‘ya‘yanta dan abin nan da ta koya, da shi za ta yi amfani ta tallafawa ‘ya’yan nata har ma da wasu.
Wadanne abubuwa ne suka ba ki sha’awa har kika assasa wannan cibiya?
Gaskiya zan ce iyayena ne, duka biyu mahaifina da mahaifiyata. Mahaifina yana da makaranta, kuma tun da na taso na gan shi, makarantarsa kamar ta sadaka ce zan ce, domin za ka ga mutum yana da ‘ya‘ya biyar, amma biyu yake biyawa, ukun kuma suna karatu ne kyauta. Tamkar dai abin da ake yi yanzu na gudummawar karatu ‘Scholarship’. A kullum mun taso mun ga mahaifinmu yana tallafawa mutane, haka ma babata, aikin kenan taimako. Shi ya sa ma ba zan iya cewa ga lokacin da na soma wannan tafiya ba saboda kawai na taso ne na ga na fara.
A Kaduna cibiyar ke gudanar da ayyukanta ko har da wasu jihohin?
Muna da sassa a wurare daban-daban, ba kawai a Kaduna muke gudanarwa ba. Muna da rassa a Zamfara, muna da shi a Kano, muna da shi a Sakkwato, da Katsina da kuma Abuja sannan da babban ofishinmu na Kaduna. Muna tafe ne a hankali muna kara fadadawa. A hankali muke kara samun mutanen da su ma suna son su ci gaba da wannan aikin tallafi, da haka muke fadadawa a wasu wuraren.
Mukan fuskanci matsalolin rashin tallafi daga jama’a, saboda duk wanda za ka tallafawa, dole sai ka yi amfani da kudi, mu yawancinmu muna aiki, da kudadenmu muke amfani wajen tallafawa. Sai kuma akwai wani shiri da muka gabatar na ‘Skill Ackuisition’ na ba mata horon sana’o’i, akwai wani mutum da ya ba mu tallafi na kekunan dinki, shi ne wanda ya taba fitowa ya ba mu tallafi. Amma duk yawancin abubuwanmu da kanmu muke yi. Idan sauran ba su da shi, ni nake bayarwa, musamman bisa la’akari da yanayin da aka tsinci kai yanzu, na babu. Sai ya zama dan kankanin abun da muke da shi, da shi muke tallafawa don ganin mun canza wa marasa karfi rayuwa. Kuma muna kokarin fita mu nunawa mutane irin ayyukanmu don su taimaka, saboda wannan aikin sadaka ne.
Wadanne fannoni kike ganin kun fi bukatar a tallafa muku?
Eh to, gaskiya akwai fannoni da yawa. Na daya akwai shiri da muka yi na ‘No Hunger Feeding Campaign, shi wannan na abinci ne, saboda mun yarda da cewa bai kamata wani ya kwana da yunwa ba, kowa ya kamata ya samu abin da zai ci ya kuma ciyar da ‘ya‘yansa. Wannan shirin muna zuwa ne gari-garin da ba su ma san mu ba, mu ma ba mu san su ba, da kuma kauyukan da ba mu taba tunanin za mu shiga ba. Idan ka ba mutum abinci ya ci ka gama masa komai.
Da haka ne muke iya samun damar shawo kan iyaye har mu sanya ‘ya’yansu a makaranta. Idan ka ba su abinci, za su aminta da kai. Idan muka ga ‘ya‘yansu muka tambaye su me ya sa ba su zuwa makaranta, sai su ce ai ba su da yadda za su yi, sai mu ce musu to su ba mu damar sanya su a makaranta. Su kan kuma amince mana. Kenan mukan samu nasarar yin abubuwa a lokaci daya.
Wasu matsalolin sai mun shiga kauyuka muke gano su, wasu lokutan da hawaye muke fitowa daga wuraren da muke zuwa. Akwai ranar da muka raba shinkafa a Kudancin Kaduna, watanni uku kafin bikin ista ‘Easter’. Sai wata yarinya take cewa mahaifiyarta, yau za su ci shinkafa, yau za su ci shinkafa. Sai mahaifiyar ta ce mata ai shinkafar nan daure ta za a yi sai da bikin ista za a dafa a ci. Sai ista fa aka ce, ka ga kenan mutane na cikin wani irin hali. Har yau ana kirana ana godiya akan wannan tallafi.
To irin wadannan abubuwan muna rokon mutane da su rika tallafawa, a rika taimakawa mutane. Akwai kuma maganar makarantar yara mata, muna bi muna janyo su da magana mai dadi, muna kuma koya musu sana’o’in hannu; irinsu saka, dinkin tabarma, dinkin sutura, yanzu ma mun samu wacce ta ce za ta koyawa matan kimiyyar kwamfuta.
Mu abin da muke so, ba kawai ka zo ka ba mu kudi ba, mutum na iya zuwa ya ba mu kayan aiki, wanda za mu koya musu sana’o’i. Wanda kai-tsaye za ka ga amfanin tallafin da ka bayar saboda anan take mutanen za su amfana da su.
A karshe wane sako gare ki ga wadanda kuke tallafawa?
A kodayaushe ina cewa don yau ba ka san da mutum ba, ya zo ya tallafa maka, ya kamata ne kai ma ka yi kokarin ganin ka taimakawa wani. Ba ki sanni ba, amma na zo na ba ki, ke ma ki nuna mini wannan abin ya shige ki, ta hanyar tallafawa na kasa da ke. A haka sai alheri ya rika zagayawa tsakanin al’umma. Akwai matar da ta yi wannan a Zariya, an ba ta kayan yin sana’ar kosai. An gayyace ni amma ban samu zuwa ba, sai dai aka dauko mana hotuna, bayan ta dan yi karfi sai ta siyo buhun wake da kayan yin kosai ta tallafawa wata ita ma da ke da matsala, wannan abu ya yi matukar burge ni. Akwai wadanda muka ba su dubu dai dai kowanne, su ma suna yin sana’o’i kanana a gida, su ma sun yi matukar jin dadi, domin da shi suke taimakawa kawunansu. Kodayaushe muna ce musu a ci gaba da tallafawa juna, don a rage samun matsaloli a tsakankanin mata.