Gwamnan Jihar Abia Okezie Ikpeazu ya ba da umarnin kafa kwamitin shari’a domin bincikar ta’asar da ake zargin ’yan sanda da aikatawa a jihar.
Ya yi alkawarin kudi ga duk wanda ya taimaka wa kwamitin binciken da bayanai game da bata-garin da suka kwace bindigogi da harsasai daga hannun ‘yan sanda a garin Aba a ranar Laraba.
Ikpeazu ya sanar da hakan ne a jawabinsa ga al’ummar jihar ranar Alhamis inda ya bayyana goyon bayansa kan korafinsu a kan jami’an ‘yan sanda a jihar.
Gwamnan ya ce an kafa kwamitin ne domin bincike da gurfanar da ‘yan sandan da aka samu da laifin cin zali.
“Kowa ya san jihar Abia ba ta goyon bayan zalunci, kuma ba za mu goyi bayan zaluncin da aka yi wa masu zanga-zangar lumana ba”, inji shi.
Ya tabbatar wa masu zanga-zangar cewa gwamnatinsa za ta yi duk abin da ya kamata wajen kare rayukansu da dukiyoyinsu.