✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ighalo ya kafa tarihi a Manchester United

Dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo ya kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya buga wa kungiyar Manchester United wasa daga…

Dan wasan gaba na Najeriya Odion Ighalo ya kafa tarihi a matsayin dan wasa na farko da ya buga wa kungiyar Manchester United wasa daga Najeriya.

Dan wasan ya buga wasa na farko da aka kara a ranar Litnin a tsakanin United  da Chelsea inda United ta ci Chelsea 2-0.

Duk da cewa minti biyu zuwa uku ya buga, wannan bai hana cewa Ighalo ya cimma burinsa na zama dan Najeriya na farko da ya buga wa Manchester United wasa ba.

Tsofaffin ’yan wasan Najeriya irin su Nwankwo Kanu na daga cikin wadanda suka bayyana cewa irin yadda Ighalo ke da burin buga wa United wasa wannan ba karamar dama ba ce bisa la’akari da halin da kungiyar take ciki a yanzu.

Kafar labarai ta BBC Hausa ta ruwaito cewa, wannan tarihi ya ja hankalin masana kwallon kafa ganin cewa United babban kulob ne a duniya, haka ma Najeriya na daya daga cikin kasashen da kungiyar ke da dimbin magoya baya a duniya.

Sunan Ighalo na daga cikin mau’du’an da suka ja hankali kwarai da gaske a shafin Twitter sakamakon yadda aka rika tattaunawa a kansa.

Tun a makon jiya kocin Manchester United Ole Gunnar Solkjaer ya bayyana cewa Ighalo na cikin ’yan wasan da za su buga masa wasa a karawa da Chelsea a gasar Premier ranar Litinin.

Ighalo mai shekara 30, ya koma United daga kungiyar Shanghai Shenhua ta China inda zai yi wasa a matsayin dan wasan aro zuwa karshen kakar bana.