✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan ’yan siyasa suka cika alkawuransu talakawa za su sami sa’ida – Sulaiman Kiyana

Honurabul Sulaiman Jubrin Kiyana daya ne daga cikin Kansiloli uku ’yan Arewa da suka ci zabe a Legas inda ya mayar da hankali wajen bai…

Honurabul Sulaiman Jubrin Kiyana daya ne daga cikin Kansiloli uku ’yan Arewa da suka ci zabe a Legas inda ya mayar da hankali wajen bai wa talakawa da gajiyayyu da sauran mabukata tallafi a yankin da ya fito na Obalande a Legas.

A watannin baya, Sulaiman Kiyana ya ba da tallafi ga wadansu gajiyayyu da tsofaffi da marasa lafiya domin rage musu radadin rayuwa inda ya bai wa mata da dattawa 150 da ke yankin tallafin Naira dubu biyar-biyar kuma ya bai wa wadansu marasa lafiya mutum 3 tallafin Naira dubu 20 kowannensu domin su kula da lafiyarsu.

Kansilan na Obalande ya shaida wa Aminiya cewa ya bai wa wadansu daga cikin al’ummar da yake wakilta wannan tallafi ne domin rage musu radadin talauci, “Wadannan mutane su ne suka fito suka zabe mu a cikin ruwa da rana mazansu da matansu da dattawa da marasa lafiya, don haka ne na zauna na yi tunani na bullo da wannan tsari domin in ba su gudunmawata koda kuwa babu yawa domin da babu gara babu dadi. Don haka a karon farko na bai wa mutum 100 tallafin Naira dubu biyar-biyar, sannan na bai wa wadansu mutum 50, kuma na bai wa wadansu marasa lafiya uku tallafin sayen magani na Naira dubu 20 kowannensu,” inji shi. Ya ce “Wadannan jama’a su suka tsaya mana, don haka dole ne mu yi musu kyakyawan wakilci, na yi ta fadi kafin in kai ga nasara har Allah Ya sa naci zabe, don haka zan tabbatar na yi amfani da damata don in kyautata rayuwar al’ummar da nake wakilta da dan abin da Allah Ya hore min.”

Ya ce idan sauran kansiloli da shugabannin kananan hukumomi da wakilan majalisun jihohi da na tarayya kowanensu zai bullo da hanyar tallafa wa jama’arsa, talakawa za su samu sauki, “Idan ’yan siyasarmu suka yi kokarin cika alkawuran da suka yi wa talakawa a lokacin yakin zabensu to jama’a da dama za su samu sa’ida su samu saukin radadin talauci,” inji shi.

Ya yi kira ga ’yan Arewa mazauna Kurmi su rika shiga harkokin siyasa ana damawa da su, kada su zamo sai dai su tura mota ta tashi ta bade su da hayaki, “Misali ni ma sai da na sha gwagwarmaya na tsaya ba sau daya ba, ba sau biyu ba ina faduwa amma daga baya Allah Ya ba ni nasara yanzu haka ni ne Shugaban Masu Rinjaye na Karamar Hukumar Etiosa, don haka dole ne mutum ya zamo mai hakuri da juriya tare da kulla kyakkyawar alaka da jama’a kafin ya kai ga nasara,” inji shi.