✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Idan muka je saro kaya da tsoffin kudi ba a karba – ’Yan kasuwar Gombe

Sun roki CBN ya kara wa’adin

Yayin da wa’adin daina karbar tsoffin kudade ke dada karatowa, mazauna Jihar Gombe da kananan yan kasuwa sun roki a kara wa’adin saboda karancin sabbin kudaden.

A ranar 31 ga watan Janairu ce dai wa’adin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya diba na daina amfani da tsofaffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200 zai cika.

Sai dai a cewar mazauna Jihar, rashin sabbin kudaden ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Wani mai sana’ar sayar da kayan marmari a garin Gombe, Ali Ahmadu, ya ce shi har yanzu bai ga sabuwar takardar kudin da idanunsa ba, musamman ta N200.

Sai dai ya ce ya ga N1,000 da 500 a hannun mutane. Ya kuma ce har zuwa Alhamis da yage kasa da mko guda a daina karbar tsoffin kudaden, su yake hada-hada da su.

Ya ce yana da iyalai kuma sana’arsa karama ce wacce yake mu’amula da kananan kudi, amma ba sa samuwa balle manyan.

Ali ya ce hakan ya sa ya fara shiga mawuyacin hali.

Ya kara da cewa ana iya zuwa da manyan kudi a yi sayayya, amma sai dai ya ba da canjin tsofaffin kudi, kuma a hakan ma canjin ba ya samuwa.

Dan kasuwar ya ce hakan ta sa suke shan wahala kuma kayansu ba sa sayuwa domin idan suka ce sai sabon kudi, babu su a kasa, idan kuma suka karbi tsohon in sun je saro wasu ba a karba.

Shi ma Maikano Audu wanda ke sana’ar POS, ya ce yanzu haka ya rufe wajen saboda babu sabbin kudi kuma ko a bankin ba sa samu saboda su kananan kwastomomi ne.

Mai kano, yace yanzu idan suka karbi tsoffin kudin, idan suka je shigarwa suna shan wahala, don haka ya zama dole su rufe shagunansu.

Wani mazaunin gari, Malam Abubakar Danjuma, kokawa ya yi da cewa idan suka je cire kudi a inda suke da sabbin, ana yi musu karin cajin kudin da kashi 100.

“A baya idan muka je cire N5,000 zuwa N10,000 cajin N100 muke biya, amma a yanzu kuma ya koma N500,” in ji Malam Abubakar.

Daga nan sai ya bukaci CBN da ya tausaya wa ’yan Najeriya ta hanyar kara wa’adin.

“Ya kamata wa’adin ya zama irin na lokacin Jonathan, domin har yanzu takardar Naira 100 ta mulkinsa da aka canja tana nan kuma ana amfani da ita.”

Hakazalika, shi ma wani mai shagon tireda a cikin unguwa, Ibrahim Bala, ya ce zai rufe shagonsa sai komai ya daidaita, saboda idan ya tara tsoffin kudin kuma ba a kara lokaci ba ya kasa shigar da su banki zai yi asara.