✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan mijina ya gaza bayan shekara 4, kada ku sake zabensa —Matar Tinubu

Mata za su samu kaso mai tsoka muddin Tinubu/Shettima suka kafa gwamnati.

Mai dakin dan takarar Shugaban Kasa na jamiyyar APC, Sanata Oluremi Tinubu, ta shawarci yan Najeriya da kada su sake zaben mijinta a karo na biyu idan ya gaza tabuka komai bayan shekara hudu.

Oluremi ta yi wannan kira ne a wajen gangamin yakin neman zaben Tinubu/Shettima na matan shiyyar Kudu maso Gabas wanda ya gudana a Owerri, babban birnin Jihar Imo.

Ta ce, “A ajiye batun addini a gefe, ni Kirista ce. Ko kun taba tunanin cewa wata rana za a samu ‘yan takara Kirista da Kirista?

“Me ya kamata ya zama madogara? Tun da mun jarraba ‘yan takara Musulmi da Kirista, bari mu jarraba wannan ma mu gani sannan bayan shekara hudu idan ba su tabuka komai ba kuna iya yin waje da su,” in ji ta.

Ta kara da cewa, bai kamata addinin mutum ya zama abin damuwa a sha’anin zabe a Najeriya ba, maimakon haka kamata ya yi a yi la’akari da tsoron Allah da dan takara ke da shi.

Saboda a cewarta, “Idan ana da mutum mai tsoron Allah, ba wai Kirista ko Musulmi ba, amma dai mutum mai tsoron Allah. Idan mai tsoron Allah ya kasance rike da mulki zai ba ku kulawar da ta dace.

A matsayinta na wadda ta yi wa Najeriya hidima a matsayin matar Gwamna da kuma Sanata, Oluremi ta bai wa matan Najeriya tabbacin za su samu kaso mai tsoka muddin Tinubu/shettima suka kafa gwamnati.

“Yanzu lokacin yi wa Najeriya aiki ne. Ba wasa muke ba. Za mu tuna da mata kuma ina ba ku tabbacin cewa Asiwaju zai tuna da ku.

“Tinubu/Shettima na da kyakkyawan tanadi ga matasa. Za mu yi aiki da kowace shiyya a kan bukatunta,” in ji Oluremi.

Da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen taron, Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, ya yi kira ga matan shiyyar Kudu maso Gabas da su yi farar dabara sannan su zabi dan takarar shugabancin kasa na APC a zabe mai zuwa.