Rahotanni da ke fitowa a kafofin watsa labaran wasanni a yanar gizo sun nuna akwai yiwuwar dan kwallon Golden Eaglets Kelechi Iheanacho ya koma kulob din Sporting Lisbon da ke Fotugal.
Kafar sadarwar allnigeriasoccer.com ta kalato cewa akwai yiwuwar kulob din FC Porto da ke Fotugal wanda tun farko shi ya fara nuna sha’awarsa a kan Kelechi Iheanacho ya rasa dan wasan bayan kulob din Sporting Lisbon ya yunkuro don ganin ya dauke shi ko ta halin ka-ka.
Yayin da kulob din Porto ya taya Kelechi a kan Yuro dubu 250, shi kuwa kulob din Lisbon ya yanke shawarar taya shi ne a kan Yuro dubu 300 a kwantaragin da zai shafe tsaron shekara hudu yana buga wa kulob din kwallo. Haka kuma kulob din ya amince ya ba mahaifin dan kwallon watau Mista James Iheanacho zunzurutun Yuro dubu 300 kwatankwacin Naira miliyan 84 idan Kelechin ya sanya wa kulob din hannu.
Rahoton ya ce tuni wakilan Iheanacho da suka fito daga kulob din Taye Academy suka tattaunawa da wakilan kulob din Sporting Lisbon da ke Fotugal don ganin an cimma matsaya.
Idan za a tuna, Kelechi Iheanacho ya ziyarci Ingila a makon jiya don sanya hannu a kulob din Manchester City amma hakan ba ta yiwu ba saboda tangardar da aka samu a yarjejeniyar da hakan ta sa dan kwallon ya koma Najeriya ba tare da ya sanya wa kulob din hannu ba.
Idan Iheanacho ya koma Fotugal mahaifinsa zai samu kason Naira miliyan 84
Rahotanni da ke fitowa a kafofin watsa labaran wasanni a yanar gizo sun nuna akwai yiwuwar dan kwallon Golden Eaglets Kelechi Iheanacho ya koma kulob…
