✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan ba za ku iya samar da wuta ba ku sayar da kamfanoninku-Osinbajo

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya fada wa kamfanonin raba wutar lantarki su saka hannun jari a hada-hadar kasuwancinsu don samun riba ko su sayar…

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya fada wa kamfanonin raba wutar lantarki su saka hannun jari a hada-hadar kasuwancinsu don samun riba ko su sayar da kamfanonin idan ba za su iya tafiyar da kamfanonin ba.
Mataimakin shugaban kasar ya yi furucin ne yayin da yake mayar da martani da kiran da shugaban kamfanin Heirs Holding Limited, Mista Tony Elumelu, ya yi a babban taron tattalin arzikin Najeriya da aka yi inda ya nemi gwamnatin tarayya ta sanya hannun jari a kamfanonin raba wutar lantarki.
Farfesa Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya ba ta da kudin da za ta sake sanya wa a cikin jarin kamfanonin raba wutar.
Ya kara da cewa su masu kamfanonin su nemi hanyoyin da za su sami karin jarin ga kasuwancinsu.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana da kashi 40 na hannun jarin kamfanonin sannan kuma masu kamfanonin suna da kashi 60 cikin dari.