Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Karamar Hukumar Birni ta Jihar Kano, Sha’aban Ibrahim Sharada, ya ce idan a yanzu aka sake gudanar da zabe a Kano jam’iyyar APC za ta fadi warwas .
Sha’aban Ibrahim Sharada, ya bayyana wa sashen Hausa na BBC cewa jam’iyyar APC a jihar Kano na kara fadawa cikin matsala, wanda hakan ne yasa suka dauki matakin da ya dace.
- Sheikh Abduljabbar ya soki lauyansa a gaban kotu
- Za a girke jiragen yaki 3 da ’yan sanda 34,500 a zaben Anambra
Sharada ya ce farin jinin APC ya disashe a jihar Kano kuma, “In yau za a yi zaben gwamna a Kano, APC faduwa za ta yi, mu kuma hakan ne ba ma so.”
Ya kuma yi karin haske kan ziyarar da suka kai ofishin uwar jam’iyyar APC da ke Abuja a ranar Laraba.
“Mun fadi abubuwa guda uku, gaba daya zaben da ake cewa an yi daga bangaren gwamnati na shugabannin jam’iyya daga kananan hukumomi da mazabu, mun yi watsi da shi kuma ba mu san da shi ba.
“Saboda an dora mutanen da ba su cancanta ba, an cire mutanen da suka dace,” inji Sharada.
Kazalika, ya bayyana zaben a matsayin rashin adalci wanda ya ce ya tilasta wasu gudanar da nasu zaben na daban.
Ya bayyana cewa shi da mutanen da suka kai wa shugaban rikon jam’iyyar, Mai Mala Buni, ziyara sun nesanta kansu daga zaben da gwamnatin jihar Kano ke shirin gudanarwa ranar Asabar.
“Da yawa daga cikin ’yan Majalisar Jihar Kano, har ma da mutanen da ke aiki da gwamnati kamar kwamishinoni, idan ka kebe da su suna fadin maganganu marasa dadi. Mu dai so muke a gyara don lokaci bai kure ba.”
Sai dai Sharada ya musanta zargin da ake na cewa makarkashiya suke wa gwamnatin ta jihar Kano.
“In da so muke ta bare wadannan jajirtattun mutane da suke cikin wannan tafiya da sai su goya wa gwamnan Kano, su yi shiru har sai lokacin zabe, kamar yadda ragowar ’yan uwanmu suka yi shiru,” a cewarsa.