✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ICPC ta rufe haramtattun makarantu 62 masu bayar da shaidar digiri

Hukumar ta ce ta rufe wani sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) na bogi da ta bankado

Hukumar Yaki da Rashawa da Sauran Laifuffuka (ICPC) ta ce ta rufe haramtattun manyan makarantu 62 a fadin Najeriya.

Kazalika, hukumar ta ce ta rufe wani sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) na bogi da ta bankado.

Hukumar ta ce ta daukin matakin rufe wuraren ne a matsayin wani bangare na kokarin da take yi na yaki da rashawa a fannin ilimin kasar nan.

Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen taron matasan da hukumar ta shirya a Abuja kan rashawa a manyan makarantu.

Da yake jawabi bisa wakilcin babbar jami’a a hukumar, Hannatu Mohammed, Owasanoye ya ce tuni an dauki matakin da ya dace a kan wadanda ke da hannu a wuraren da aka rufen.

Ya ce ICPC ta kafa kwamiti na musamman a makarantu domin yaki da rashawa, musamman a manyan makarantu.

Ya kara da cewa, kwamitin kan yi kokarin horar da mambobinsa kan nesanta kansu da rashawa da kuma cusa kyawawan dabi’u a zukatan takwarorinsu dalibai.

A nasa bangaren, babban mai jawabi a wajen taron, Farfesa Williams Barnabas, ya nuna bukatar bincikar dalibai masu son shiga manyan makarantu domin tabbatar da suna da cancantar da ake bukata.