Hukumar Yaki da Rashawa da Sauran Laifuffuka (ICPC) ta ce ta rufe haramtattun manyan makarantu 62 a fadin Najeriya.
Kazalika, hukumar ta ce ta rufe wani sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC) na bogi da ta bankado.
- Likita 1 ke kula da lafiyar ’yan Najeriya 8,300
- Birtaniya ta horar da matan Najeriya 16,000 kan fasahar zamani
Hukumar ta ce ta daukin matakin rufe wuraren ne a matsayin wani bangare na kokarin da take yi na yaki da rashawa a fannin ilimin kasar nan.
Shugaban ICPC, Farfesa Bolaji Owasanoye, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a wajen taron matasan da hukumar ta shirya a Abuja kan rashawa a manyan makarantu.
Da yake jawabi bisa wakilcin babbar jami’a a hukumar, Hannatu Mohammed, Owasanoye ya ce tuni an dauki matakin da ya dace a kan wadanda ke da hannu a wuraren da aka rufen.
Ya ce ICPC ta kafa kwamiti na musamman a makarantu domin yaki da rashawa, musamman a manyan makarantu.
Ya kara da cewa, kwamitin kan yi kokarin horar da mambobinsa kan nesanta kansu da rashawa da kuma cusa kyawawan dabi’u a zukatan takwarorinsu dalibai.
A nasa bangaren, babban mai jawabi a wajen taron, Farfesa Williams Barnabas, ya nuna bukatar bincikar dalibai masu son shiga manyan makarantu domin tabbatar da suna da cancantar da ake bukata.