✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ICPC ta kama matar da ke sayar da sabbin kudi a Twitter

Hukumar na ci gaba da bincike don gano wadanda ke yi wa tsarin zagon kasa.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Kasa (ICPC) ta kama wata mata mai shafin Twitter mai suna @Simisola, kan zargin ta da sayar da sabbin takardar kudin Naira a shafukan sada zumunta.

Kakakin hukumar, Misis Azuka Ogugua a wata sanarwa a ranar Laraba, ta ce an kama matar ne sakamakon bayanan sirri da jami’an ICPC suka bankado.

“Ana zargin tana hada baki da wasu wajen karkatar da sabbin kudi daga bankuna zuwa kasuwar bayan fage,” in ji ta.

Ta ce wadda ake zargin ta yi amfani da yanayin karancin sabbin takardun Naira wajen tallata hajarta a shafinta.

 

Ta kara da cewa matar, wadda ’yar kasuwa ce a dandalin sada zumunta, tana sayar da mayukan gyara jiki, kasuwancin man fetur, harkar sufuri da sauran harkokin kasuwanci.

A cewarta, wadda ake zargin a halin yanzu na tsare a hannun ICPC kuma tana taimaka wa hukumar wajen gano masu hannu a karancin sabbin kudaden da aka sauya wa fasali.

Ta bayyana kamun a matsayin wani shirin hadin gwiwa tsakanin CBN, ICPC da EFCC wajen aiwatar da sabon tsarin sauya fasalin takardun Naira.