✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ICC za ta fara sauraron shari’ar aikata laifukan yaki a Sudan

Za a fara sauraron shari'ar bayan shafe shekara 20 ana dakon lokaci.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), za ta fara sauraron shari’a kan zargin aikata laifukan yaki a Sudan shekara 20, bayan rikicin kasar da ya hallaka dimbin fararen hula.

Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman da ke matsayin tsohon jagoran mayakan sa-kai na kungiyar Janjaweed, na fuskantar tuhume-tuhume guda 31,  ciki har da laifukan yaki da na cin zarafin bil Adama da ya kunshi fyade, azabtarwa da kuma tsangwama ga wasu al’ummar kasar.

Lauyan kare hakkin dan Adam na Sudan Moassad Mohamed Ali, ya bayyana ranar fara wannan shari’a a matsayin mai cike da farin cikin ga dubban wadanda yakin ya shafa don tabbatar musu da adalci.

Masu shigar da kara ga kotun ta ICC sun bayyana Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushyab a matsayin babban kwamandan Janjaweed da ya jagoranci dubban mayakan kungiyar tsakanin 2003 zuwa 2004 wajen aikata kashe-kashe mafi kololuwar muni a lokacin rikicin Darfur.

Sai dai Abd-Al-Rahman, ya musanta dukkanin zarge-zargen masu shigar da karar a kansa, inda a lokuta da dama shi da lauyoyin da ke kare su ke ci gaba da ikirarin cewa an yi kuskuren tuhumarsa da laifukan da wani daban ya aikata.

A cewar lauyoyin tsohon jagoran na Janjaweed umarnin da ya bayar a wancan lokaci ba shi da masaniyar zai kai ga aikata laifukan yaki.

A watan Yunin 2020 ne Abd-Al-Rahman, ya mika kansa ga kotun da ke da birnin Hague shekara 13 bayan shelanta nemansa kan zargin aikata laifukan yakin.