Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), za ta fara sauraron shari’a kan zargin aikata laifukan yaki a Sudan shekara 20, bayan rikicin kasar da ya hallaka dimbin fararen hula.
Ali Muhammad Ali Abd-Al-Rahman da ke matsayin tsohon jagoran mayakan sa-kai na kungiyar Janjaweed, na fuskantar tuhume-tuhume guda 31, ciki har da laifukan yaki da na cin zarafin bil Adama da ya kunshi fyade, azabtarwa da kuma tsangwama ga wasu al’ummar kasar.
- ‘Likitoci 9,000 sun bar Najeriya cikin shekara 2’
- Ramadan: Zulum ya ninka wa ma’aikatan wucin gadi a Borno albashinsu sau uku
Lauyan kare hakkin dan Adam na Sudan Moassad Mohamed Ali, ya bayyana ranar fara wannan shari’a a matsayin mai cike da farin cikin ga dubban wadanda yakin ya shafa don tabbatar musu da adalci.
Masu shigar da kara ga kotun ta ICC sun bayyana Abd-Al-Rahman, wanda aka fi sani da Ali Kushyab a matsayin babban kwamandan Janjaweed da ya jagoranci dubban mayakan kungiyar tsakanin 2003 zuwa 2004 wajen aikata kashe-kashe mafi kololuwar muni a lokacin rikicin Darfur.
Sai dai Abd-Al-Rahman, ya musanta dukkanin zarge-zargen masu shigar da karar a kansa, inda a lokuta da dama shi da lauyoyin da ke kare su ke ci gaba da ikirarin cewa an yi kuskuren tuhumarsa da laifukan da wani daban ya aikata.
A cewar lauyoyin tsohon jagoran na Janjaweed umarnin da ya bayar a wancan lokaci ba shi da masaniyar zai kai ga aikata laifukan yaki.
A watan Yunin 2020 ne Abd-Al-Rahman, ya mika kansa ga kotun da ke da birnin Hague shekara 13 bayan shelanta nemansa kan zargin aikata laifukan yakin.