kwallayen biyun da dan kwallon Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Zlatan Ibrahimobic ya zura a ragar kulob din Nantes a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin Faransa (French League Cup) a ranar Talatar da ta wuce ta sa kulob din ya haye wasan karshe.
Ibrahimobic, dan asalin Sweden, ya zura kwallon farko ne a farkon rabin lokaci sai dai minti tara kafin a tashi wasan dan kwallon Nantes Olibier biegneau ya fanshe cin da aka yi musu.
A daidai minti na 90 Zlatan Ibrahimobic ya zura kwallo ta biyu da kai a raga da hakan ta jefa daukacin magoya bayan kulob din cikin murna.
“Gaskiya mun ji dadin wannan nasara da muka samu da ta ba mu kai wa wasan karshe”, inji Ibrahimobic dan kimanin shekara 32 a lokacin da yake hira da ’yan jarida jim kadan bayan an tashi wasan.
Ibrahimobic ya kai kulob din PSG wasan karshe
kwallayen biyun da dan kwallon Paris Saint Germain (PSG) da ke Faransa Zlatan Ibrahimobic ya zura a ragar kulob din Nantes a wasan kusa da…